Sanatan APC Ya Jawo Magana, Ya Bukaci Masoyansa Su 'Kashe' Abokan Hamayya

Sanatan APC Ya Jawo Magana, Ya Bukaci Masoyansa Su 'Kashe' Abokan Hamayya

  • Wani Sanata daga Osun ya jawo ce-ce-ku-ce bayan an zarge shi da umartar magoya bayansa su kashe ’yan jam’iyyar Accord
  • Mawakin Afrobeats, Davido, ya wallafa bidiyon Sanatan yana magana da Yarbanci, tare da bayyana cewa ya yi kira ga magoya baya su kai wa Accord hari
  • Zargin ya zo ne kwanaki kadan kafin zaben gwamnan Osun, yayin da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki ke kira ga ’yan siyasa su guji tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Wani Sanata da ke wakiltar daya daga cikin mazabun Sanatoci na Osun ya jawo ce-ce-ku-ce bayan malamansa.

Ana zargin sanatan da kiran magoya bayansa su kashe ’yan jam’iyyar Accord gabanin zaben gwamna na ranar Asabar.

Sanatan APC ya tayar da kura kan zaben jihar Osun
Taswirar jihar Osun da ake shirin zabe. Hoto: Legit.
Source: Original

Bidiyon sanatan APC na barazana a Osun

Kara karanta wannan

PDP ta yi sabon ango, dan majalisa a Kano ya watsar da jam'iyyar Abba Kabir

Dan jam’iyyarAPC ya yi kalaman a wani bidiyo da mawaki, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Mawaki Davido, wanda ya wallafa bidiyon, ya bayyana Sanatan a matsayin wanda ke kan kujerar Sanata, sannan ya fassara kalaman Sanatan daga Yarbanci zuwa Turanci.

A cewar fassarar da Davido ya wallafa, Sanatan ya ce:

“Daga yanzu, duk lokacin da kuka ga ’yan Accord, ku kashe su. Na ba ku izinin kashe su. Suna da mata da ’ya’ya ma.
“Wannan zaben na gwamnatin tarayya ne. A ranar zabe, ko da sun zo da katunan zabe, ba za mu bari su kada kuri’a ba.”

A cikin bidiyon, an ga mutumin yana jawabi ga magoya bayansa da harshen Yarbanci, yayin da yake magana kan jam’iyyar Accord da zaben da ke tafe.

An taso sanatan APC a gaba kan bidiyon kisan kai
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da tambarin jam'iyyar APC. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Source: Twitter

An caccaki sanatan APC kan kalamansa

Wadannan kalaman da ake zargin Sanatan ya yi sun zo ne kwanaki kadan kafin al’ummar Osun su fito rumfunan zabe domin zaben sabon gwamna.

A wani bangare na jawabin, bisa ga fassarar, Sanatan ya ce:

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke fasto da sojoji kan shirya sace matan manyan malaman addini a Plateau

“Wace irin rayuwa ce wannan? Idan muka ji wani abu game da Accord a nan Ilesa, ku dauki bidiyo na ku je ku fada musu.
“Idan muka gaya musu, hular da suke sanyawa ba ta dace ba, hula ce mai launin rawaya.
“Saboda haka, mun zo ne domin mu fada muku yanzu, daga yau har zuwa ranar zabe, idan muka gan su, ku kashe su.”

Idan aka tabbatar da cewa an fassara kalaman yadda ya kamata kuma an gabatar da su cikin mahallin da ya dace, hakan na iya kara fargabar tashin hankalin siyasa da tsoratar da masu kada kuri’a a Osun.

Rahoton ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a tantance cikakken yanayin da aka yi kalaman da kuma sahihancin fassarar kafin daukar matakin karshe kan zargin.

An kashe wani yaro a Osun

Mun ba ku labarin cewa an samu tashin hankali a Ilesa da ke jihar Osun, bayan an harbi wani yaro mai suna Tobi Ilesanmi, yayin gangamin APC.

Shaidu sun ce harsashi ya same shi ne a cikin shagon mahaifiyarsa, yayin da ake ta harbe-harbe a lokacin jerin gangamin jam’iyyar.

Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce an kama Kwamishinan Muhalli, Mayowa Adejoorin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.