Yan ta'adda
Yan bindiga sun tashi hankulan jama'ar wani yanki a jihar Kwara bayan miyagun sun kai wani hari a gidan Sarki inda suka sace ƴaƴansa guda uku yayin farmakin.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan rahotannin da ke cewa tantirin dan bindiga, Bello Turji, ya mika wuya. DHQ ta ce ana ci gaba da farautarsa.
Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai hari a Kauran Namoda, ya yi Allah wadai da kisan da ake cigaba da yi wa al'umma.
Wasu 'yan bindiga da ke biyayya ga Bello Turji sun kai farmaki a Sokoto, inda suka kashe mutum daya, suka sace wasu 16, duk da batun sulhu da ubangidansu.
Rigima ta barke tsakanin manyan yan bindiga bayan Kachalla Alti ya kashe hatsabibin dan bindiga Dankarami Usaini a kauyen Matsuki, Zamfara, bayan rikicin nuna iko.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci rundunar sojojin saman Najeriya da ta kara zafafa kai hare-hare kan 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP.
A labarin nan, za a ji cewa wani Mai Unguwa a Katsina, Salisu Abdullahi ya shaida wa jami'an tsaro yadda ya ke jan 'yan ta'adda don kai hari kauyuka.
Ana ta mayar da martani kan maganar tattaunawa da Bello Turji tsakanin malamai yayin daMurtala Bello Asada ya mayar da martani ga Sheikh Adam Muhammad Albaniy.
A labarin nan, za a ji cewa jama'a a jihar Sakkwato sun shiga firgici a lokacin da 'yan ta'adda su ka bude wuta a kan wasu masallata da su na sallar Asuba.
Yan ta'adda
Samu kari