'Yan Ta'addan ISWAP Sun Hallaka Manoma da Masunta a Jihar Borno
- Ƴan ta'adda na kungiyar ISWAP ɗauke da makamai sun huce fushinsu a kan wasu manoma da masunta a jihar Borno
- Miyagun sun hallaka mutane sama da 20 bisa zarginsu da haɗa kai da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da suke gaba da ita
- An kai wannan mugun harin ne yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar hare-haren ta'addanci a garuruwan Borno
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan ta'addan ISWAP sun hallaka aƙalla manoma da masunta 23 a wani hari da suka kai a jihar Borno.
Ƴan ta'addan ISWAP sun kai harin ne da safiyar ranar Alhamis a ƙauyen Malam Karanti, wani yanki mai nisa da ke kusa da Baga a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Asali: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan ta'addan ISWAP sun yi ɓarna a Borno
Ƴan ta'addan na ISWAP sun kai harin ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla tsakanin mutanen yankin da ƴan Boko Haram.
Majiyoyi da mazauna yankin sun bayyana cewa mafi yawan waɗanda aka kashe manoman wake ne daga Gwoza, waɗanda a baya sun cimma yarjejeniyar zama lafiya da wani ɓangare na Boko Haram.
Sun ƙulla yarjejeniyar ne domin su samu damar noma da kamun kifi a cikin yankunan da yan ta’addan ke iko da su, da sharaɗin za su riƙa biyan haraji akai-akai.
Sai dai ƙauyen Malam Karanti, wanda ke kimanin kilomita 60 daga garin Baga, na ƙarƙashin ikon wani ɓangare daban na ISWAP wanda aka fi sani da tsananin sanya dokar iko a yankunan da ke ƙarƙashinsa.
Wani ɗan sa-kai ya bayyana cewa mayaƙan sun shigo ƙauyen Malam Karanti da misalin ƙarfe 9:00 na safe, suka tattara manoma da masunta, suka kashe mutum 23 bisa zargin suna haɗa kai da Boko Haram.
“‘Yan ta’addan sun bar wani tsoho da rai, wanda daga baya ya koma cikin gari ya bayyana abin da ya faru. Sun zargi waɗanda suka kashe da haɗa kai da Boko Haram da kuma sabawa dokar ISWAP."
"Mafi yawansu manoman wake ne daga Gwoza da ke biyan haraji ga Boko Haram domin su yi amfani da filin noma."
- Wani ɗan sa-kai

Asali: Original
Ƴan ISWAP sun hana a ɗauko gawarwaki
Ƙoƙarin ceto gawarwakin ya ci tura saboda mayaƙan sun dawo suka bude wuta kan mutanen da suka je ɗauko su, lamarin da ya tilasta musu janyewa.
“Mun yi kokarin haɗa kai da jami’an tsaro domin dauko gawarwakin, amma ‘yan ta’addan sun dawo suka hana mu. Yanzu haka iyalai da dama na jiran gawar ƴan uwansu."
- Wata majiya
Malam Karanti na daga cikin wuraren da ISWAP ke da karfi sosai, kuma duk da haɗarin da ke tattare da hakan, fararen hula da ke cikin ƙuncin rayuwa na shiga irin waɗannan wurare domin noma da kamun kifi saboda tsananin talauci da ƙarancin abinci.
Sojoji sun ragargaji ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi gumurzu da ƴan ta'addan Boko Haram a jihar.Borno.
Sojojin sun samu nasarar fatattakar ƴan ta'addan daga maɓoyarsu da ke cikon dajin Sambisa a artabun da suka yi.
Hakazalika, jami'an tsaron sun ƙwato.makamai masu tarin yawa bayan ƴan ta'addan sun tsere zuwa cikin daji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng