Sarkin Zazzau Ya Yi Kira a Rage Kudin da ake Kashewa yayin Bukukuwa

Sarkin Zazzau Ya Yi Kira a Rage Kudin da ake Kashewa yayin Bukukuwa

  • Mai martaba Sarkin Zazzau ya buƙaci 'yan Najeriya su rage kashe makudan kuɗi yayin bukukuwa, su rika taimaka wa talakawa maimakon haka
  • Sarkin ya shawarci iyaye su hana 'ya'yansu kashe kuɗi masu dimbin yawa wajen kwalliya da sayen atamfa da sunan anko a lokacin bukukuwa
  • Ya ce ya kamata a karkatar da irin kuɗi wajen taimaka wa mabukata ko a rika miƙa su ga ƙungiyoyin da ke tallafa wa talakawa a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya shawarci iyaye da su gargadi 'ya'yansu kan kashe kuɗi masu yawa wajen kwalliya da anko a lokacin bukukuwan aurensu.

Da yake jawabi a bikin cika shekara 20 na kungiyar Musulmai ta CMO, a Abuja, Sarkin ya ce ya kamata a yi amfani da irin waɗannan kuɗi wajen taimaka wa mabukata.

Kara karanta wannan

Tuban muzuru: Malami ya gargadi gwamnati game da karban tuban yan bindiga

Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli
Sarkin Zazzau yana bayani a wajen taron CMO a Abuja
Source: Facebook

Korafin kan kashe kuɗi a biki

Daily Trust ta rahoto cewa Sarkin Zazzau ya nuna damuwa cewa duk da matsin tattalin arzikin da ake ciki a ƙasar nan, mutane da dama na ci gaba da kashe kudi masu yawa a harkokin biki.

“Za ka ga mutanenmu suna kashe miliyoyin Naira kan kayan kwalliya idan za a yi wa yarinya aure, saboda akwai wasu iyaye da ba su da hankali da suke kashe har dala 10,000 kan kwalliyar da ake yi. Ko kuma su sayi atamfar anko ta N500,000 ko N200,000 ko N300,000 wanda a gare ni sam ba abin yarda ba ne.”

Sarkin ya nemi a taimaki talaka

A cikin bayanin da ya yi, mai martaba Sarkin Zazzau ya bukaci a rika taimakon talakawa da irin kudin maimakon kashe su a biki.

Ya ce:

“Akwai mutane da yawa da ba sa iya samun abinci sau uku a rana. Hakan ya yawaita a cikin al'ummarmu. Amma wasu daga cikinmu mun ɗauki matsaya.

Kara karanta wannan

Sokoto: Jama'a sun shiga firgici da 'yan bindiga suka kashe limami da wasu mutane

"Ni ban taɓa kashe ko sisi wajen anko ko kayan kwalliyar amarya ba. Idan mahaifiyarta ta zaɓi yin haka, wannan ra'ayin ta ne. Ko kuma idan wani yana son yin haka, ya yi, amma ni ba zan kashe ko sisi ba.”
“Mutane suna kashe kuɗi masu yawa wajen bukukuwa da ba su da wani muhimmanci. Ba na cewa kada a yi biki, amma akwai abubuwan da ya kamata mu rage.
"Dole mu faɗawa kanmu gaskiya. Ba ma buƙatar irin waɗannan abubuwa idan aka yi la'akari da halin da ƙasar ke ciki a yanzu.”
Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli da wasu malamai
Dr Jabir Sani Mai Hula, Dr Muhammad Salah da Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli a wajen taro a Abuja. Hoto: Zazzau Emirates
Source: Facebook

Kiran Sarkin Zazzau ga jama'a

Bayan korafi game da yadda abin da jama'a ke yi, Sarkin ya bukaci al'umma su mayar da hankali kan abubuwan da za su amfane su.

Trust Radio ya rahoto ya ce:

“Saboda haka, ina roƙonku da ku mai da hankali kan abubuwan da za su inganta rayuwarku, su sa ku dogara da kanku, kuma su ƙarfafa haɗin kai a cikin al'umma.
"Domin idan kana rayuwa cikin yalwa, amma mutanen da ke kewaye da kai ba sa iya samun abinci sau uku a rana, ina ganin akwai matsala, kuma wannan ne ke jefa mu cikin haɗari a cikin al'ummarmu.”

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kawo hanyar magance rikicin manoma da makiyaya

Nafisat ta soki zaman aure

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo muku cewa jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi ta caccaki mata kan zaman aure.

Jarumar ta bayyana cewa zaman aure bautar maza ne saboda haka kwata-kwata ba ta shirya zama baiwa a gidan wani ba.

Nafisat Abdullahi ta shawarci mata da su yi kokarin gina rayuwarsu wajen kama sana'a da dukkan hanyoyin da suka dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng