Rashin Tsaro: Gwamna Zulum Ya Ayyana Ranar Yin Azumi da Addu'a a Borno

Rashin Tsaro: Gwamna Zulum Ya Ayyana Ranar Yin Azumi da Addu'a a Borno

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi bayani kan irin ƙoƙarin da yake kan matsalar rashin tsaro
  • Zulum ya nuna cewa gwamnatinsa na haɗa kai da gwamnatin tarayya domin ganin an kawo ƙarshen matsalar
  • A bisa hakan ya buƙaci mutanen jihar da su ɗauki azumin nafila a ranar Litinin da yin addu'o'i kan rashin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ayyana ranar gudanar da azumi saboda matsalar rashin tsaro.

Gwamna Zulum ya ayyana ranar Litinin a matsayin rana ta yin azumin nafila da addu'a a faɗin jihar.

Gwamna Babagana Umara Zulum
Gwamna Zulum ya sanya ranar yin azumi a Borno Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Gwamnan ya sanar da hakan ne a cikin jawabin da ya gabatarwa al’umma baki ɗaya a Maiduguri a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙoƙarin da Zulum ke yi kan rashin tsaro

Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙudiri aniyar ƙarfafa rundunar sa-kai, inganta tattara bayanan sirri a matakin ƙauyuka, domin magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

“A watannin baya-bayan nan, na gudanar da muhawara da dama tare da abokan haɗin gwiwarmu na gwamnatin tarayya da kuma shugabannin hukumomin tsaro daban-daban."
"Ina farin cikin sanar da ku cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin jihar Borno da gwamnatin tarayya ta ƙarfi fiye da baya."
"A tare, muna aiki kan tsare-tsare na haɗin gwiwa domin ƙarfafa tsarin tsaro, inganta musayar bayanan sirri, da kuma ba jami’an tsaro kayan aiki da dabaru da suka dace domin tinkarar barazanar da ke gabanmu."

- Farfesa Babagana Umara Zulum

Gwamnan ya sake jaddada cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tabbacin cewa zai tunkari ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta ba tare da jinkiri ba, rahoton jaridar ThePunch ya tabbatar.

“Lallai, gwamnatin tarayyar Najeriya, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da dukkan manyan hafsoshin tsaro, sun ba mu tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da muke fama da ita a jihar nan."

“A bisa la’akari da halin da muke ciki a fannin tsaro, ina kira ga daukacin mazauna Jjhar Borno da mu haɗu a matsayin ƴaƴa na gari cikin aiki na imani da haɗin kai."

- Farfesa Babagana Umara Zulum

Jihar Borno
Zulum ya sa ranar yin azumi a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yaushe za a yi azumi a Borno?

"A ranar Litinin, ina gayyatar kowa da kowa da ya ɗauki azumin nafila da yin addu'a domin neman zaman lafiya a jihar Borno, yankin Arewa Maso Gabas da kuma ƙasa baki ɗaya."
"Mu haɗu domin neman jagoranci daga Ubangiji, samun waraka da kwanciyar hankali a jiharmu."

- Farfesa Babagana Umara Zulum

Ya kamata a koma ga Allah

Mazaunin jihar Borno, Muhammad Kabir, ya shaidawa Legit Hausa cewa ya kamata a koma ga Allah don samun mafita kan matsalar rashin tsaron.

"Wannan shawara ce mai kyau ta yin azumi don samun mafita kan matsalar rashin tsaro."
"Muna fatan mutane makwabtanmu za su taya mu yin addu'o'i don mu samu sauƙi daga wajen Allah."

- Muhammad Kabir

Zulum ya kafa dokoki a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanar da sababbin dokoki guda biyu.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya haramta sare itatuwa ba bisa ƙa'ida ba a faɗin jihar Borno.

A cikin sabuwar dokar akwai tanadin biyan tara ko zama a gidan gyaran hali ga waɗanda aka samu da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng