Sojoji Sun Kashe Babban Abokin Bello Turji bayan Luguden Wuta Suna Shirya Taro
- Daya daga cikin manyan abokan kasurgumin ɗan ta’adda Bello Turji ya rasa ransa a wani farmakin sojojin sama a jihar Sokoto kwanan nan
- Sojojin sama na Operation Fansan Yamma ne suka kai farmakin a maboyar 'yan ta’adda kusa da makarantar Tunfa a ƙaramar hukumar Isa
- Rundunar soji ta ce dan ta'addan da aka kashe, Shaudo Alku na da alaƙar samar da makamai da shigo da kayan yaƙi daga Nijar zuwa ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Shaudo Alku, babban abokin ɗan ta’adda Bello Turji, a wani farmakin sama da aka kai maboyar 'yan ta’adda a jihar Sokoto.
An kai farmakin ne a ranar Lahadi ta hannun dakarun sama na Operation Fansan Yamma, wanda ya auka a kusa da makarantar firamare ta Tunfa, da ke ƙaramar hukumar Isa.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kashe dan ta'addan ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan sirri sun nuna cewa Alku ya shigo Najeriya daga jamhuriyar Nijar don halartar wata ganawar sirri da bangaren Turji ya shirya.
An kashe abokin Bello Turji, Shaudo Alku
Rundunar soji ta bayyana Alku a matsayin mutum mai muhimmin matsayi wajen samar da makamai da haɗa kai da mayakan Turji daga ƙasashen waje.
Punch ta rahoto cewa wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
“Mun samu bayanan sirri da suka tabbatar da inda suke taro, hakan ya sa muka kai hari cikin gaggawa wanda ya yi nasarar hallaka masu taron.”
Ya ƙara da cewa hallaka dan ta'addan babbar nasara ce wajen rushe tsarin jagoranci da haɗin guiwar 'yan ta’adda a Arewacin Najeriya.
An kashe 'yan ta'adda tare da abokin Turji
Rundunar ta ce bayan Alku, harin ya hallaka wasu kwamandoji da dama da kuma mayaka da ake zargin suna cikin jiga-jigan 'yan ƙungiyar Turji.
Sojojin sun bayyana wannan nasara a matsayin alamar ƙudurinsu na kawar da 'yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a jihohin da rikici ya fi shafa kamar Sokoto, Zamfara da Katsina.
An kuma bayyana cewa ana ci gaba da aiwatar da aikin kammala hare hare da kuma farautar sauran mayakan da suka tsere.

Asali: Twitter
Bello Turji na daga cikin fitattun shugabannin 'yan ta’adda da suka fi tayar da hankali a Arewacin Najeriya, inda ya jima yana da hannu a sace-sacen mutane da kashe-kashe.
Sojoji sun fatattaki Boko Haram a Sambisa
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki kan 'yan ta'addan Boko Haram a dajin Sambisa.
Rahoton da rundunar soji ta fitar ya nuna cewa an fatattaki 'yan Boko Haram da dama da suke zaune a dajin.
Baya ga fatattakar 'yan ta'addan, sojojin sun kwato makaman da Boko Haram ke amfani da su wajen ka hare hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng