A ƙarshe, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Shugaban APC da Suka Yi Garkuwa da Shi

A ƙarshe, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Shugaban APC da Suka Yi Garkuwa da Shi

  • Yan bindiga da suka sace shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ose a Ondo, Nelson Adepoyigi, sun kashe shi
  • Kakakin shugaban karamar hukumar Ose ya ce maharan sun sako mutanen da suka kai kudin fansa, amma sun kashe Adepoyigi cikin daji
  • Rundunar 'yan sanda na ci gaba da bincike a daji don gano gawar, yayin da iyalai da ‘yan siyasa ke jimamin wannan mummunan kisan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Akure, Ondo - An tabbatar da cewa shugaban APC da yan bindiga suka kama a jihar Ondo ya rasa ransa.

Maharan sun hallaka Nelson Adepoyigi wanda suka sace a karamar hukumar Ose ta jihar duk da biyansu kudin fansa.

Yan bindiga sun kashe shugaban APC
Yan bindiga sun hallaka shugaban APC da suka sace. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ondo: Yan bindiga sun hallaka shugaban APC

Clement Kolapo Ojo, shugaban karamar hukumar Ose, ya tabbatar da rasuwar Adepoyigi a wata sanarwa da aka fitar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ojo, cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Oluwaseun Ogunniyi ya fitar, ya ce an kashe shugaban APC din ne yayin da maharan suka sako mutanen da suka kai kudin fansa.

Ya ce:

“Muna godiya da cewa an sako masu kai kudin fansa biyu, amma abin bakin ciki ne cewa maharan sun kashe Mista Nelson Adepoyigi da gangan.
”Dukkan shugabanni da al’ummar karamar hukumar Ose na cikin jimamin wannan babban rashi, muna mika ta’aziyyarmu ga dangi da abokan siyasa na mamacin."

Wani jami'in dan sanda ya yi magana

An kasa samun kwamishinan ‘yan sanda Wilfred Afolabi domin jin ta bakinsa a ranar Lahadi 18 ga watan Mayun 2025.

Sai dai wani babban jami’in ‘yan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa yan jaridu cewa jami’an tsaro na cikin daji suna neman gawar Adepoyigi.

“Eh, gaskiya ne an kashe shi, amma jami’anmu suna cikin daji suna kokarin gano gawarsa."

- Cewar jami’in dan sanda

An kashe shugaban APC
Yan sun hallaka shugaban APC a Ondo. Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Yadda yan bindiga suka addabi jihar Ondo

Adepoyigi, wanda shi ne shugaban APC na mazabar 5 a Ifon, an sace shi ne da yammacin Litinin a kofar gidansa kan hanyar Ifon/Owo.

Masu garkuwar sun fara neman N100m a matsayin fansa kafin iyalansa su nemi alfarma daga maharan inda suka sassauta zuwa N5m, cewar Premium Times.

A shekarar 2023 ma, wasu ‘yan bindiga sun kashe Bola Adelegbe, dan’uwan Hon. Timileyin Adelegbe, dan majalisar wakilai mai wakiltar Owo/Ose.

An sace Bola a Ose, kuma an kashe shi a sansanin masu garkuwa da mutane duk da an biya kudin fansa.

Ɗan APC ta tattauna da Legit Hausa

Wani dan APC a Gombe, Ibrahim Fari ya ce lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace kan miyagun yan bindiga.

"Idan ma a baya ana ganin abin ba komai ba to yanzu an hallaka shugaban APC kuma a kwanaki na wani jigonta ya mutu a hannun yan bindiga."

- Cewar Fari

Ya shawarci al'umma su rika ba da hadin kai ga jami'an tsaro domin kawo karshen ta'addanci a fadin ƙasar.

Yan bindiga sun kama masu kai kudin fansa

A wani labarin yan bindiga sun tsare mutanen da suka kai kudin fansar shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo, Nelson Adepoyigi.

An sace Adepoyigi da ke shugabantar jam’iyyar a gundumar Ifon ne a kofar gidansa da ke kan hanyar Ifon zuwa Owo, aka kai shi cikin daji.

Bayan an rage kudin fansa daga makudan kudi N100m zuwa N5m, masu garkuwan sun tsare wadanda suka kai kudin domin kubutar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.