Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram, an Tura 'Yan Ta'adda zuwa Barzahu

Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin Boko Haram, an Tura 'Yan Ta'adda zuwa Barzahu

  • Dakarun sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar mafarauta sun samu nasarar daƙile wani harin ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Jami'an tsaron sun fatattaki ƴan ta'addan tare da kashe wasu daga cikinsu bayan sun kai hari a ƙauyen Warambe da ke ƙaramar hukumar Gwoza
  • Bayan fatattakar ƴan ta'addan, jami'an tsaron sun kuma samu nasarar ƙwato wasu makamai a hannun miyagun da suka yi shekaru suna ta'adi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Sojoji tare da haɗin gwiwar mafarauta sun daƙile wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a ƙauyen Warambe da ke ƙaramar hukumar Gwoza, jihar Borno.

A yayin arangamar, jami'an tsaron sun samu nasarar kashe mayaƙan Boko Haram guda biyar.

Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram
Dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Shugaban ƙungiyar mafarauta a yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙauyen Warambe na ɗaya daga cikin sababbin ƙauyukan da aka maido da mazauna cikinsu bayan an kori ƴan ta’adda daga yankin.

Sai dai mayakan Boko Haram sun sha ƙoƙarin sake shigowa ƙauyen domin aiwatar da munanan ayyuka.

Shugaban mafarautan ya ce mayaƙan sun farmaki ƙauyen ne da safiyar ranar Juma’a da misalin ƙarfe 6:00 na safe.

"Amma tawagata ta yi gaggawar mayar da martani, inda muka yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram guda biyar. Mun ƙwato bindigogi da harsasai daga hannunsu, waɗanda a halin yanzu ke hannun dakarun sojoji."

- Shugaban mafarauta

Sanata Ndume ya yabawa sojoji

Sanata Mohammed Ali Ndume (APC, Borno Kudu), ya jinjinawa dakarun sojoji da kuma mafarautan bisa yadda suka daƙile harin cikin gaggawa.

Sanata Mohammed Ali Ndume
Ndume ya yabawa dakarun sojoji Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume
Asali: Twitter

Ya ce wannan namijin ƙoƙarin ya ƙarawa mazauna yankin ƙwarin gwiwa da samun natsuwa a zukatansu.

“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa an kashe mayaƙan Boko Haram guda biyar a Warambe."

"Ina yabawa da jajircewar mafarauta da kuma yadda dakarun sojoji na Operation Hadin Kai suka gaggauta kai ɗauki, wanda hakan ya taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin."

- Sanata Mohammed Ali Ndume

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da aka kori mayaƙan daga ƙauyen, an ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu da harsasai, kuma an mika su ga sojoji don ci gaba da bincike.

Wannan nasara wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke yi na daƙile ayyukan ƴan ta’adda a yankunan da ke fama da rikici a Arewa maso Gabas, tare da tabbatar da dawowar zaman lafiya da walwala ga al’umma.

Ƴan ta'addan ISWAP sun hallaka manoma

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan ISWAP ɗauke da makamai sun hallaka wasu manoma da masunta a jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun hallaka manoman ne bayan sun zarge su da haɗa baki da ƴan ƙungiyar Boko Haram.

Tsagerun sun kai harin ne dai a ƙauyen Malam Karanti da ke ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng