Bayan Ɗauke Sarki Har cikin Fadarsa, Ƴan Bindiga Sun Koma Garin, Sun Yi Ta'asa

Bayan Ɗauke Sarki Har cikin Fadarsa, Ƴan Bindiga Sun Koma Garin, Sun Yi Ta'asa

  • Yan bindiga sun kuma kai hari a jihar Kogi inda suka kashe matasa uku da ake zargin ‘yan sa-kai ne a Ofoloke
  • Majiyoyi sun ce matasan ‘yan sa-kan an dauke su ne don kare ma’aikatan sadarwa da suka je gyara na’urar sadarwa a daji
  • Wani matashi, Demola Samuel, ya ce al’umma na cikin fargaba da damuwa, dole ne a dauki matakan tsaro, mutane na barin yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Yan bindiga sun kuma kai hari a jihar Kogi inda suka hallaka wasu matasa guda uku.

Maharan sun kashe matasa uku da ake zargin su ne masu farauta da aikin sa-kai a garin Ofoloke da ke karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar.

Yan bindiga sun kashe mutane 3
Yan bindiga sun kai hari a Kogi. Hoto: Legit.
Asali: Original

Daily Trust ta ce an harbe matasan ne ‘yan kwanaki bayan wasu gungun ‘yan bindiga sun shiga fadarar wani sarki suka sace shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan bindiga suka sace basarake a Kogi

An sace Mai martaba sarkin Ofoloke, HRM Ogunyanda Ilufemiloye ne da safiyar ranar Alhamis 15 ga watan Mayun 2025 da ta gabata.

An ce maharan sun kutsa fadar Sarkin inda suka ci zarafin fadawa kafin suka ɗauke basaraken suka yi awon gaba da shi.

Har yanzu babu wani labari game da halin da Sarkin ke ciki yayin da al'umma ke cikin zulumi.

Yan bindiga sun hallaka matasa a Kogi

Wani dan yankin ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari da safiyar Asabar inda suka kashe matasa uku.

Wata majiyar daban ya ce an kashe su ne a wani kwanton-bauna yayin da suke bincike a daji don gano inda aka kai sarkin yankin.

Majiyar ta ce:

"Wannan tashin hankali da aka yi kwanan nan ya jefa mu cikin bakin ciki. Mun rasa rayuka uku a yankin nan bayan sace sarki."

Yan bindiga sun kai hari a Kogi
Bayan sace Sarki, yan bindiga sun kuma kai hari a Kogi. Hoto: Ahmed Usman Ododo.
Asali: Facebook

Menene yan sanda suka ce kan harin?

Wani shugaban matasa a yankin, Demola Samuel ya bayyana babban tashin hankali da suka shiga sanadin harin.

Ya ce:

“Wannan tashin hankali ya wuce misali kuma yana nuna cewa akwai bukatar matakan tsaro na gaggawa.
“An ga gawarwakin matasan uku a daji da safiyar Asabar, hakan ya kara tayar da hankalin al’ummar yankin.
“Yankinmu na cikin hali na tsaka mai wuya; mutane na barin garin saboda tsoron abin da zai biyo baya."

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa kiran waya ko sakon karta-kwana da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

An zargi jirgi da ba yan bindiga makamai

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta musanta rade-radin cewa jirgin sama ya kai kayan abinci ko makamai ga 'yan bindiga a jihar Kogi.

Rundunar ta bayyana cewa jirgin ya shiga aikin yaki da 'yan bindiga tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da yan banga a Obajana.

Jami'an sun bukaci jama’a da su daina yarda labaran karya, su rika sauraron bayanai daga hukumomin tsaro tukuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.