Sanata Ndume Ya Yaba da Jarumtar Sojoji kan Boko Haram, Ya ba Su Kyauta
- Sanata Ali Ndume ya ƙarawa dakarun sojoji ƙarfin gwiwa wajen tunkarar ƴan ta'addan Boko Haram masu tayar da ƙayar baya
- Ndume wanda ya yaba bisa daƙile hare-haren ƴan ta'addan da jami'an tsaron suka yi, ya ba su kyautar shanu da kuɗi a jihar Borno
- Sanatan na Kudancin Borno ya buƙaci jami'an tsaron da su ci gaba da nuna juriya da jajircewa a yaƙin da suke yi da ƴan ta'addan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Sanata Ali Ndume ya yabawa dakarun sojoji, ƴan sa-kai na CJTF da mafarauta wajen daƙile hare-haren Boko Haram a ƙauyukan Izge da Yamtake na ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Sanata Ali Ndume ya ba da kyautar shanu guda uku da kuma Naira miliyan biyu, domin su yi murnar nasarorin da suka samu a kan ƴan ta'addan.

Asali: UGC
Sanata Ali Ndume ya yabawa dakarun sojoji
Sanata Ndume ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake miƙa tallafin ga wadanda suka ci gajiyarsa a ƙauyukan Izge da Yamtake, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Gwoza, Hon. Ibrahim Abba Chukun ya wakilta, ya samu rakiyar wasu manyan mutane daga yankin, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Idan ba a manta ba ƙauyukan Izge da Yamtake na daga cikin wuraren da Boko Haram suka kai hari, inda aka samu asarar rayuka daga ɓangaren sojoji da ƴan ta'addan.
Daga ƙarshe dakarun sojoji sun rinjaye su tare da ƙwato makamansu kafin su gudu zuwa maɓoyarsu a dajin Sambisa.
Wace kyauta Sanata Ndume ya yi?
Ya bayyana cewa shanun guda uku an ba da su ne ga mafarauta/CJTF na Yamtake da Izge, sannan ɗaya kuma ga dakarun gwamnati waɗanda suka nuna jarumta a Izge.
Haka kuma ya ce, za a raba Naira miliyan biyu tsakaninsu domin su samu sayen kayan miya don yin murnar nasarorin da suka samu.

Asali: Twitter
"A cikin irin karamcinsa, Sanatanmu Mohammed Ali Ndume ya ba da gudunmawar shanu guda uku da kuma Naira miliyan biyu domin a raba tsakanin dakarun sojoji, mafarauta da ƴan sa-kai da suka daƙile harin Boko Haram a ƙauyukan Izge da Yamtake na ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.”
"Sanata Ndume ya kuma umarce ni da na yaba da jarumtakar dakarun sojoji, mafarauta, ƴan sa-kai da sauran jama’a suka nuna a cikin waɗannan ƙauyuka wajen fuskantar Boko Haram, tare da bukatar su ci gaba da jajircewa, domin a cewarsa, zaman lafiya aikin kowa ne."
- Hon. Ibrahim Abba Chukun
Zulum ya yi jimamin hare-haren Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna alhininsa kan hare-haren da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai.
Gwamna Zulum ya yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a sababbin hare-haren na ƴan ta'addan.
Hakazalika ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da gwamnatin tarayya domin ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng