Ardo Risku: Mutane 10 da Ake Zargi da Kisan Shugaban Miyetti Allah Sun Shiga Hannu
- Rundunar 'yan sandan Benue ta kwantarwa al'umma hankali game da binciken da ake yi na kisan shugaban Miyetti Allah da abokinsa
- Yan sanda sun ce an kashe mamatan ne yayin da suke dawowa daga taron tsaro a Ohimini, inda 'yan sanda suka fara bincike
- Kwamishinan 'yan sanda ya tabbatar da ci gaba da bincike, yana mai alkawarin kamo sauran masu hannu a lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Rundunar yan sanda a Benue ta bayyana nasarar da ta samu game da bincike kan hallaka shugaban Miyetti Allah a jihar.
Rundunar ta ce ta kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan shugaban ƙungiyar na Benue, Alhaji Ardo Risku Mohammed, da abokinsa Yakubu Isah.

Source: Facebook
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, DSP Udeme Edet, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a Makurdi, cewar Punch.
Yan sanda sun kama wadanda ake zargi
An kashe Ardo Risku da Yakubu Isah ne a kan hanyar karkara ta Okwudu-Okpachenyi da ke ƙaramar hukumar Otukpo, yayin da suke dawowa daga taron tsaro da aka gudanar a ƙaramar hukumar Ohimini.
Rundunar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a daren Asabar bayan wani samame da jami'an rundunar suka gudanar bisa bayanan sirri a ƙaramar hukumar Otukpo.
Ta ce kamen ya biyo bayan bincike mai zurfi da tattara bayanan sirri tare da ayyukan jami'an tsaro da aka fara nan take bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban MACBAN da abokinsa.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Titus Thyodenda mai shekara 25, Utibe Sam mai shekara 20, Owoicho Ameh mai shekara 18, Sunday Useni mai shekara 21 da Sunday Ogbanje mai shekara 46.
Sauran sun haɗa da Daniel Raphael mai shekara 23, Adokole John mai shekara 24, Samuel Ogazi mai shekara 32, Agbo Daniel mai shekara 25 da Onazi James mai shekara 30.

Source: Original
Yan sanda sun sha yabo daga kwamishina
Kwamishinan 'yan sandan Benue, CP Cletus Nwadiogbu, ya yaba wa jami'an bincike da na rundunar musamman saboda saurin ɗaukar mataki da ƙwarewar da suka nuna, wanda ya kai ga cafke waɗanda ake zargi.
Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa bincike na ci gaba, tare da ƙara ƙaimi wajen gano da kuma kamo sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a wannan kisan.
Kwamishinan ya sake jaddada kudirin rundunar na tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa tanadin doka.
Ya kuma roƙi al'umma su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da ba jami'an tsaro haɗin kai tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kammala binciken.
Risku: Gwamna ya kadu da kisan shugaban MACBAN
An ji cewa Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah-wadai da kisan shugaban MACBAN na Benue, Alhaji Ardo Risku da dan uwansa.
Alia ya ce kisan ya faru ne a lokacin da zaman lafiya ke kara dawowa a sassan Benue, yana mai cewa hakan barazana ce ga kokarin sulhu.
Gwamnan ya umarci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike, su kamo masu hannu a kisan tare da tabbatar da an hukunta su.
Asali: Legit.ng


