Kungiyar Kirisrocin Najeriya CAN
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami kafatanin manyan shuwagabannin hukumomin tsaron Najeriya gaba dayansu sakamakon cigaba da tabarbarewar tsaro da ake samu a Najeriya.
Kungiyar gwamnonin Arewa ta yi Allah-wadai da kisan Reverend Lawan Andimi, wanda ya kasance Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na gida kuma babban fasto a yankin Michika, jihar Adamawa wanda kungiyar yan ta’adda ta yi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III tare da shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Samson Olasupo za su gana a wani babban taro da zai gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu.
Fadar Shugaban kasa ta fada ma kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) cewa siyasantar da addini bai da gurin zama a Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta haramta.
A karon farko an samu coci a gidan wannan Gwamnan na Arewacin Najeriya bayan shekaru 28. Yahaya Bello ne ya bude wani katafaren coci a fadar Gwamnati a makon jiya.
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, ta jinjina ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa tirjiyar data nuna wajen yaki da kokarin kakaba ma yan Najeriya auren jinsi guda da turawa ke kokarin yi.
Ranar Litinin din nan ne Ikhide Ikheloa, wanda aka fi sani da PA Ikhide, ya caccaki mutanen yankin Afirka akan yadda suka yadda da littafin Bible. Ikhide ya bayyana cewa "Bible rubutu ne kawai na tatsuniyar gizo da koki da wasu...
Tun ranar Lahadi 21 ga watan Oktoba yake cikin wardrobe bayan barkewar rikicin Kaduna, inda ya boye don gudun kada a kasheshi, amma masu gidan basu san yana ciki ba, har sai da na tsinceshi a ciki. Anan na dauke shi tunda ba zai i
Kungiyar al’ummar kiristocin Arewacin Najeriya ta mika kokon bararta ga kungiyar ta’addanci na Boko Haram game da cigaba da rike wata daliba guda daya tak da suka sace tare da sama da dalibai dari daga makarantar yan mata ta Dapch
Kungiyar Kirisrocin Najeriya CAN
Samu kari