Sarkin Musulmi da shugaban kiristoci za su tattauna kan mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya

Sarkin Musulmi da shugaban kiristoci za su tattauna kan mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III tare da shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Samson Olasupo za su gana a wani babban taro da zai gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu.

Daily Trust ta ruwaito makasudin wannan taro shi ne tattauna halin da Najeriya take ciki. Wannan na daga cikin abubuwan da zasu gudana a yayin taron kungiyoyin addinai na Interfaith Dialogue Forum for Peace (IDFP) karo na 3.

KU KARANTA: Lamari ya ta’azzara: Duk wanda suka zalunce mu Allah Ya tsine musu albarka – Kwankwaso

Shuwagabannin kungiyar, Alhaji Ishaq Kunle Sanni da Bishop Sunday Onuoha ne suka bayyana haka yayin da suke ganawa da manema labaru a Abuja a ranar Talata, 21 ga watan Janairu, inda suka ce akwai dalilin farin ciki a Najeriya, duk da kalubalen da ake fuskanta.

Shuwagabannin biyu sun bayyana cewa akwai cigaba a bangaren tsaro a Najeriya, duk da matsalolin da ake fuskanta. Sa’annan sun tabbatar da bukatar baiwa kowanne dan Najeriya yancin aiwatar da addininsa yadda ya kamata.

A wani labarin kuma, a kokarinsa na rage matsalar cin hanci da rashawa, shugaban hukumar kwastam, Alhaji Hamid Ali ya umarci jami’an hukumar kwastam da su dinga bayyana adadin kadarorinsu a kowanne shekara daga bana.

Ali ya sanar da haka ne a ranar Talata, 21 ga watan Janairu yayin da jami’an hukumar da’ar ma’aikata, CCB, suka kai masa ziyara a ofishinsa a karkashin jagorancin shugaban hukumar, Mohammed Isah.

“Dokar hukumar kwastam ta bukaci duk jami’an kwastam su bayyana kadarorinsu da dukiyoyinsu a duk shekara saboda irin aikin da muke yi, aiki ne na kudi, don haka dole ne mu zama abin koyi ga sauran jama’a.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel