Gwamnan Jihar Kogi ya kaddamar da coci domin ibadar Kiristoci

Gwamnan Jihar Kogi ya kaddamar da coci domin ibadar Kiristoci

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya kaddamar da cocin farko da aka taba ginawa Kiristoci a fadar gwamnatin da aka fi sani da ‘Lugard House’.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, tun shekaru 28 da aka kirkiri Kogi, sai yanzu ne aka samu coci a gidan gwamnati.

Alhaji Yahaya Bello ya yi jawabi bayan bude wannan coci a ranar makon jajibirin Kirismeti a Lokoja a Ranar Litinin 22 ga Watan Disamba.

Mataimamin gwamna watau Mista Edward Onoja, shi ne ya wakilici Mai girma gwamnan a wajen bikin bude wannan wurin ibada na Kiristoci.

Gwamnan ya bayyana cewa cocin ba ya nufin wajen bauta kawai, sai dai alama ce ta cewa gwamnatinsa za ta hada kan al’ummar jihar.

KU KARANTA: Kirismeti: Manyan Arewa sun roki Buhari ya kubutar da Leah Sharibu

“Wannan coci ya zarce makasudinsa na bauta da ibada. Cocin zai zama alamar hadin-kai da jawo kowa a jika da tafiya da kowa.” inji Bello.

Mai girma gwamnan ya godewa kungiyar Kiristoci na CAN na jihar Kogi da kuma na kasa baki daya, saboda kokarinsu wajen ganin an yi aikin.

Haka zalika Bello ya nuna godiya ga daukacin mutanen jihar da su ka mara masa baya, su ka sake zaben APC kwanaki domin ya zarce kan mulki.

Alhaji Bello ta bakin Mataimakin na sa ya yi wa Kiristocin da ke jihar Kogi fatan ayi bikin Kirisemti da sabuwar shekara mai zuwa lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel