'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Wasu Mutane
- An yi garkuwa da Sarkin gargajiya na Igbesi da wasu mazauna yankin Isin na Jihar Kwara a wani hari da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai
- Uwargidan Baale na Dabu, wadda aka fi sani da Iya Ayoka, ita ma ta fada hannun masu garkuwa da mutane
- Lamarin ya kara jefa mazauna yankunan Kwara ta Kudu cikin fargabar rashin tsaro da hare-haren 'yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Ilorin, jihar Kwara - Ana zargin wasu ‘yan bindiga da yin garkuwa da Sarkin gargajiya na al’ummar Igbesi da ke karamar hukumar Isin ta Jihar Kwara.
'Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna yankin, a wani mummunan hari da suka kai wa kauyen.

Source: Original
Harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Asabar, 22 ga watan Agustan 2026 inda maharan suka yi awon gaba da basaraken da wasu mazauna yankin zuwa wani wuri da ba a sani ba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Har zuwa ranar Lahadi, babu wani rahoton cewa masu garkuwar sun bukaci kudin fansa domin sakin wadanda suka kama.
An fara kokarin ceto sarkin
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kwara, CP Ojo Adekimi, ya tabbatar da sace basaraken, inda ya shaida wa jaridar Daily Trust a daren Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026 cewa jami’an tsaro sun fara kokarin gano inda yake domin ceto shi.
Adekimi ya ce:
“’Yan sanda suna hada kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an saki basaraken cikin koshin lafiya.”
Ya bayyana cewa har yanzu ana kokarin gano cikakken abin da ya faru, yana mai cewa saboda lokacin da aka kai harin ya yi latti, hakan ya sa ba a iya tantance adadin maharan nan take ba.
Kwamishinan ya ce jami’an tsaro sun riga sun shiga daji domin bin sawun wadanda suka aikata laifin.
Ya kara da cewa jami’ansa sun kwato wasu shanun da aka yi sata a yayin samamen, amma ya fayyace cewa shanun da aka gano ba su da alaka da sace basaraken.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai hare hare a Katsina, dubunnan mutane sun tsere daga gidajensu
Kwamishinan ya bukaci mazauna yankin da su kasance cikin taka-tsantsan tare da sanar da jami’an tsaro duk wani sahihin bayani da zai taimaka wajen gudanar da aikin ceto da kama wadanda suka aikata laifin.
An kuma sace Iya Ayoka
A wani lamarin daban, an kuma ruwaito cewa wasu da ake zargin ‘5 sun yi garkuwa da matar farko ta Baale na al’ummar Dabu da ke karamar hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara, wadda aka fi sani da Iya Ayoka.
Shugaban karamar hukumar Ifelodun, Alhaji Femi Yusuf, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun riga sun fara bin sawun masu garkuwar domin ceto matar.
Sai dai ya bayyana lamarin a matsayin abin da bai saba aukuwa ba, yana mai cewa yanayin tsaro a karamar hukumar ya samu gagarumin sauki a baya-bayan nan.
Abubuwan da suka faru a wadannan al’ummomi daban-daban na Kwara ta Kudu sun kara tayar da hankalin mazauna yankin kan matsalar tsaro.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun yi barna a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe wani jami’in rundunar hadin gwiwa (JTF), tare da yin garkuwa da wata mata mai suna Asma’u da ɗanta Umar, jihar Kaduna.
'Yan bindigan sun yi ta'asar ne a Kyauta New Millennium City da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng