Fadar shugaban ta gargadi kungiyar CAN da kakkausar murya
- Fadar Shugaban kasa ta caccaki kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) game da furucinta kan hare-haren yan ta’addan Boko Haram
- Garba Shehu ya jadadda cewa rundunar tsaron Najeriya na aiki ba ji ba gani don dawo da mutanen da Boko Haram suka kama ga iyalansu
- Shehu ya kuma yi gargadin cewa gwamnati ba za ta taba lamuntan rashin hakurin addini ba
Fadar Shugaban kasa ta fada ma kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) cewa siyasantar da addini bai da gurin zama a Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta haramta.
Kakakin Shugaban kasar, Garba Shehu, yayinda yake martani ga jawabin kwanan nan daga kungiyar CAN, ya ce gwamnati ba za ta taba lamuntan rashin hakurin addini ba.
Shehu wanda ya sake jadadda goyon bayan gwamnati kan kowa ya yi addinin da yake muradi, ya shawarci kungiyar CAN da ta yi hange mai kyau a kan matsalolin da ake fuskanta a yanzu domin kada ta fada tuggun yan ta’adda.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban jigon APC a Ondo
Ya bayyana cewa rundunar tsaron Najeriya na aiki ba ji ba gani don dawo da mutanen da Boko Haram suka kama ga iyalansu.
Ya ce gwamnati na da cikakken karfin gwiwa kan kokarinsu na cika aikin su.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng