Abin Ya Fara Yiwa Tinubu Yawa, Jigon APC Ya ba Atiku Gaskiya kan Dawo da Tallafin Fetur a Najeriya
- Wani jigon APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya goyi bayan sukar da Atiku Abubakar ya yi kan cire tallafin man fetur
- Vatsa ya ce cire tallafin ya jefa ’yan Najeriya cikin tsananin wahala tare da kara tsadar rayuwa tun bayan zuwan Tinubu
- Ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sake duba manufar tare da rage wa ’yan Najeriya radadin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Jigo a APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya goyi bayan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, kan batun tallafin mai.
Vatsa, wanda ya taba zama Kwamishinan Yada Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido na Jihar Neja, ya ce manufar cire tallafin ta jefa ’yan Najeriya cikin tsananin wahala ba tare da samar musu da wata fa’ida mai ma’ana ba.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur

Source: Twitter
Jigon APC ya goyi bayan Atiku
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna ranar Lahadi mai taken, “Mu dauki sakon Atiku, mu bar mai sakon”, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Jigon APC din ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake duba manufar cire tallafin tare da ba ’yan Najeriya hakuri kan wahalhalun da ya ce manufar ta jawo.
Vatsa ya ce bambancin siyasa tsakanin Tinubu da Atiku bai kamata ya hana Gwamnatin Tarayya yin la’akari da abin da Atiku ya fada ba.
“Ko da ba ka son mai sakon, ya kamata a kalla ka dauki sakon. Duniya baki daya ta san cewa manufar cire tallafin da wannan gwamnati ta aiwatar ta gaza; ta jefa ’yan Najeriya cikin matsanancin talauci,” in ji shi.
Me Vatsa ya ce game da tallafin?
A cewar Vatsa, manufar ta amfani gwamnonin 36, iyalansu, zababbun masu rike da mukaman siyasa da wadanda gwamnati ta nada, yayin da talakawan Najeriya ke ci gaba da fama da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan
Jigo a APC kuma dan kasuwar mai ya kwancewa Atiku zani kan dawo da tallafin fetur
Ya ce cire tallafin man fetur bai kawo wata fa’ida ga talakawa ba, illa kara jefa masu karamin karfi cikin matsalar tattalin arziki, kamar yadda Daily Post ta kawo.
“Cire tallafin man fetur ya amfani gwamnonin jihohi 36, iyalansu, zababbun masu rike da mukaman siyasa da wadanda gwamnati ta nada wadanda ke da damar samun kudaden gwamnati.
“Bai amfani talakawan da ke kan tituna ba. Ya kara jefa masu karamin karfi a Najeriya cikin matsanancin talauci. A yanzu rayuwa ta zama ba ta da ma’ana ga talakawan Najeriya,” in ji Vatsa.

Source: Getty Images
Tsohon sakataren yada labarai na APC a Jihar Neja ya bayyana ci gaba da aiwatar da manufar da ya ce ta gaza inganta rayuwar ’yan kasa a matsayin “babban jahilci”.
Ya bukaci Shugaba Tinubu ya sake tunani kan manufar cire tallafin tare da daukar matakan da za su rage wa ’yan Najeriya nauyin tattalin arzikin da suke fuskanta.
Dalilin Atiku na shirin dawo da tallafi
A wani labarin, kun ji cewa Kenneth Okonkwo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya yi karin haske kan batun dawo da tallafin mai.
Okonkwo ya ce manufar shirin ita ce rage farashin man fetur ga talakawan Najeriya, yana mai cewa ba shi da alaƙa da tsohon tsarin tallafin man fetur da aka yi amfani da shi a baya.
Asali: Legit.ng