Coronavirus: Shugaban CAN ya ce mugunta da laifuffukan jama’a ne ya haifar da annobar

Coronavirus: Shugaban CAN ya ce mugunta da laifuffukan jama’a ne ya haifar da annobar

- Rev Samson Ayokunle, Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya wato CAN ya ce mugunta da sauran laifuffuka ne suka haddasa annobar coronavirus

- Sai dai kuma Shugaban CAN din ya ce Allah na da warakar cutar ta COVID-19

- Ayokunle ya yi bayanin cewa mutane da yawa a duniya sun yi watsi da umurnin Allah a karkashin fakewa da yancin dan adam

Rev Samson Ayokunle, Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), ya ce mugunta da laifuffukan da mutane ke aikatawa sabanin abun da Allah ya yi umurni ne ya haddasa annobar coronavirus.

An tattaro cewa Rev Ayokunle ya bayyana hakan ne a wata sanarwa a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris a yayin da yake wa’azi na musamman wanda aka gudanar a gidan talbijin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa malamin ya kuma bayyana cewa Allah na da warakar cutar.

Ya ce mutane da dama a duniya sun yi watsi da umurnin Allah karkashin fakewa da yancin dan adam.

Coronavirus: Shugaban CAN ya ce mugunta da laifuffukan jama’a ne ya haifar da annobar
Coronavirus: Shugaban CAN ya ce mugunta da laifuffukan jama’a ne ya haifar da annobar
Asali: Facebook

Malamin ya ce saboda bunkasar fasaha, mutane na ganin za su iya cimma abubuwa da dama ba tare da Allah ba don haka suke ganin kansu tamkar ubangiji.

Sai dai Ayokunle ya ba yan Najeriya tabbacin cewa wadanda ke da tsoron Allah kada su sanya tsoro a zukatansu game da kowani annoba.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamnatin Kano ta karyata labarin bullar cutar a jahar

A bangare daya mun ji cewa an samu mutum na farko da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litinin, 23 ga Maris 2019.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta tabbatar da mutuwar a shafinta na Tuwita.

Jawabin ciyar yace “An samu mutuwar farko sakamakon COVID19 a Najeriya. Wani dan shekara 67 ne wanda ya dawo daga Ingila jinya.“

“Ya kasance mai fama da rashin lafiya da ciwon siga.“

Majiyarmu ta bayyana sunan mutumin matsayin, Suleiman Achigu wanda ya kasance tsohon dirakta manajan kamfanin kasuwancin man feturin Najerya PPMC.

Ya mutu misalin karfe 2 na dare a asibitin koyarwan jamiar Abuja.

An ce ya fara nuna alamun cutar ranar Talata sai aka bayyanawa cibiyar NCDC inda suka dauki jininsa domin gwaji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel