Shugaban Majalisar Dokokin Bauchi Ya Kamu da Cuta, Ya ba Jama'a Shawara

Shugaban Majalisar Dokokin Bauchi Ya Kamu da Cuta, Ya ba Jama'a Shawara

  • Cutar ido mai saurin yaɗuwa ta fara bazuwa a sassa daban-daban na Jihar Bauchi, inda Kakakin Majalisar Dokokin jihar ya ce ya kamu da ita
  • Abubakar Suleiman ya bukaci mazauna jihar su kula da tsafta tare da ɗaukar matakan kariya domin dakile yaɗuwar cutar.
  • Ana iya yaɗa cutar Apollo ta hanyar hulɗa da wanda ya kamu da ita ko ta amfani da abubuwan da suka gurɓata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Cutar ido mai saurin yaɗuwa da aka fi sani da “Apollo” ta fara yaɗuwa a Jihar Bauchi, da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Cutar ta Apollo ta ritsa da Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Abubakar Suleiman, wanda ya bayyana cewa ya kamu da ita.

Cuta ta kama shugaban majalisar dokokin Bauchi
Shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman Hoto: Abubakar Y Suleiman
Source: Facebook

Kakakin Majalisa ya kamu da cutar

Abubakar Suleiman ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara, sun tura yan bindiga da dama lahira

Ya ce ya tashi da alamun cutar, yana mai bayyana damuwa kan yadda cutar ke ci gaba da yaɗuwa a sassan jihar.

“Cikin ikon Allah, yau na tashi da ciwon ido mai saurin yaɗuwa, wadda aka fi sani da “Apollo,” kuma a halin yanzu tana yaɗuwa a faɗin jihar Bauchi." In ji shi.

An yi kira ga mazauna jihar su yi taka-tsantsan

Kakakin Majalisar ya yi kira ga mazauna Bauchi da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kula da tsaftar jiki da muhalli domin rage haɗarin yaɗuwar cutar.

Ya kuma bukaci jama’a da su ɗauki matakan kariya da suka dace domin dakile ƙarin yaɗuwar cutar a tsakanin al’umma.

Suleiman ya shawarci mazauna jihar da su kula da tsafta tare da guje wa amfani da kayan mutane, musamman abubuwan da za su iya taimakawa wajen yaɗa cutar.

"Ina kira ga kowa da kowa da ya kasance cikin taka-tsantsan, ya kula da tsafta, tare da ɗaukar matakan kariya da suka dace domin hana cutar ƙara yaɗuwa a tsakanin al’umma. Allah uban giji ya kawo mana sauki Na gode." In ji shi.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar zai dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaben 2027

Yadda Apollo ke yaɗuwa

Apollo, wadda aka fi sani da conjunctivitis, cuta ce mai saurin yaɗuwa da ke shafar ido.

Ana iya yaɗa cutar ta hanyar hulɗa da mutumin da ya kamu da ita ko kuma ta hanyar taɓa gurɓatattun wurare da kayan amfani na mutum.

Hukumar lafiya ta shawarci jama’a da su ɗauki matakan tsafta da kariya domin rage yiwuwar kamuwa da cutar da kuma hana ta yaɗuwa ga sauran mutane.

Apollo ta kama kakakin majalisar dokokin Bauchi
Abubakar Suleiman, shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi Hoto: Abubakar Y. Suleiman
Source: Facebook

Abin da ke kara yaduwar HIV

A wani labarin kuma, kun ji cewa Likitoci sun bayyana cewa karuwar sababbin masu kamuwa da cutar HIV a Najeriya na da alaƙa da raguwar tallafin kasashen waje. Masana harkokin lafiya sun kuma danganta haka da ƙarin talauci da kuma raguwar shirye-shiryen wayar da kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng