Kungiyar CAN ta yi martani ga labarin haihuwar Leah a hannun yan ta’adda

Kungiyar CAN ta yi martani ga labarin haihuwar Leah a hannun yan ta’adda

Shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya da malamai a Damaturu, babbar birnin jihar Yobe, sun nuna bakin ciki kan rahotannin cewa Leah Sharibu ta haifi ‘da namiji a tsare.

Micheal Oshomah ya bayyana cewa cigaba da tsare Leah Sharibu ya kasance abun damuwa ga al’umman Kirista wadanda basu taba gajiya ga neman a ceto ta ba.

Labaran da ke yawo ya nuna cewa Leah ta haifi ‘da namiji a tsare, lamarin da ya bata ran al’umman Kirista a jihar Yobe.

Yayinda yake martani ga lamarin, wani fasto a Damaturu, Rt. Reverend Yohana Audu ya ce ya yi bakin ciki matuka da lamarin wanda ya bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen ceto ta da dadewa. Ya kuma jadadda cewa abunda ya fi muhimmanci a yanzu shine tsaro da kuma dawowar yarinyar a kan lokaci.

Hakazalika, kungiyar kiristocin Najeriya, reshen jihar Yobe, ta bakin sakatarenta, Reverend Bright Ogbasiegbe, ya bayyana cewa basu ji dadin lamarin ba amma suna kira ga bincike sosai yayinda suke addu’an dawowarta cikin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Yan kunar bakin wake sun kashe mutane 3 a Masallaci a Borno

Duk da mummunan lamarin, kungiyar kiristocin Yobe ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da ceto Leah Sharibu.

A ranar 19 ga watan Fabrairu me Leah za ta cika shekaru biyu a hannun yan ta’addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel