Dokar hana auren jinsi: CAN ta jinjina ma shugaba Muhammadu Buhari
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, ta jinjina ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa tirjiyar data nuna wajen yaki da kokarin kakaba ma yan Najeriya auren jinsi guda da turawa ke kokarin yi.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito shugaban CAN, Samson Ayokunle ne ya bayyana haka inda yace kokarin da gwamnatin Buhari ke yi wajen haramta auren jinsi da kuma sauya halitta daga namiji zuwa mace ko mace zuwa namiji abin a yaba mata ne.
KU KARANTA: Tsantseni: Buhari ya tara kudin shiga naira tiriliyan 2 a wata 6 kacal
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ayokunle ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Adebyao Oladeji a ranar Talata, 10 ga watan Satumba a babbar birnin tarayya Abuja, inda ya koka kan yadda badala ke kara wanzuwa a Najeriya, sa’annan ya bayyana sauya halitta a matsayin haramtaccen lamari.
Sa’anann ya jinjina ma shugaban hukumar cigaban al’adun gargajiya ta Najeriya, Otunba Olusegun Runsewa bisa yadda yake yaki da miyagun ayyukan madigo, luwadi da sauya halitta a tsakanin yan Najeriya.
“Muna da yakinin duk wani mai hankali da kungiyoyi masu zaman kansu zasu hada kai da gwamnati domin kawar da wadannan miyagun ayyuka daga Najeriya saboda kundin tsarin mulkinmu da dokokinmu basu san luwadi, madigo da sauya halitta ba, haramun ne a addininmu da al’adunmu.” Inji shi.
Daga karshen shugaban na CAN ya bayyana cewa ire iren dabi’un nan zasu iya jefa kasar cikin mawuyacin hali da kuma fushin ubangiji a kan duk mutanen da suka rungumi wadannan munanan halaye.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng