Kano: Ganduje ya bude dakin gwaji na musamman don Kiristocin jihar

Kano: Ganduje ya bude dakin gwaji na musamman don Kiristocin jihar

- Domin tabbatar da yawaita gwajin kwayar cutar korona a jihar Kano, Gwamna Ganduje ya bude sabon dakin gwaji a Sabon Gari

- Gwamnan ya ce dakin gwajin na musamman ne don Kiristocin da ke jihar su samu damar yin gwajin kwayar cutar

- A cewar gwamnan, bayan an gwada su, hukumar kula da cutuka masu yaduwa za ta san matakin dauka bayan samun sakamakon

Domin assasawa da hanzarta gwajin kwayar cutar korona a jihar Kano, a jiya Talata gwamnatin jihar ta samar da sabon dakin gwaji don kiristocin jihar da ke yankin Sabon Gari na jihar.

A yayin taro da wasu daga cikin mambobin kungiyar kiristoci ta Najeriya tare da Gwamna Ganduje a gidan gwamnati, ya ce amfanin samar wa da kiristocin dakin gwajin kansu shine don su samu damar yin gwajin babu wata takura.

Ya ce dakin gwajin na nan a Sabon Gari kuma kiristoci za su iya zuwa gwajin, jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Sakamakon gwajin za a mika ga NCDC don daukar mataki na gaba, in ji Ganduje.

Kano: Ganduje ya bude dakin gwaji na musamman don Kiristocin jihar
Kano: Ganduje ya bude dakin gwaji na musamman don Kiristocin jihar. Hoto daga SaharaReporters
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya yi wa Malamai 'Allah ya isa'

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi wa malaman da suka zargesa da hana sallar Juma'a a jihar 'Allah ya isa'. Gwamnan ya ce ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga 'yan jiharsa a yammacin Talata.

A cewarsa, "Ko a makka ba za a yi sallar idi ba amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Saboda haka Allah ya isa. Na yafe wa duk wanda ya zage ni amma ba zan yafe wa wanda yayi min kazafi ba."

Gwamnan ya tabbatar da cewa ba zai bar kowanne mutum shiga jihar Kaduna a ranar Sallah daga Kano ba. Kasancewar gwamnatin jihar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma'a.

"Da kaina zan je hanyar shigowa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana. Cuta ta riga tayi katutu a tsakanin mutane. Mu kuwa ba za mu bari su shigo mana da ita ba. Ba zai yuwu ba," in ji El-Rufai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel