Yaron Ministan Tinubu Ya Tashi da Kujera da APC Ta KashedKuka mukamai 184 a zabe
- Jam'iyyar APC ce kadai ta shiga zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da aka yi a jihar Ebonyi
- Osborn Nweze Umahi, dan ministan ayyuka David Umahi, yana daya daga cikin wadanda suka yi nasara
- Yaron Umahi zai shugabanci karamar hukumar Ohaozara amma jam'iyyar PDP a jihar Ebonyi ta soki zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ebonyi - Jam’iyyar APC ta lashe duka kujerun ciyamomi 13 da ake da su da aka yi zaben kananan hukumomi a jihar Ebonyi.
A ranar Asabar da ta gabata, hukumar zabe mai zaman kanta a Ebonyi, EBSIEC ta gudanar da zaben kananan hukumomi.

Source: Facebook
Zaben da aka a gudanar a jihar Ebonyi
The Cable ta ce duka kujerun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli sun fada hannun APC mai mulki a jihar da kasa.
Shugaban EBSIEC, Enyi Patrick, a ayyana ‘yan takaran APC a matsayin wadanda za su zama ciyamomi 13 a fadin jihar.

Kara karanta wannan
Duk da suna jam'iyya 1, Gwamna Radda ya yi maganar nadin da Tinubu ya yi maaa a kwamitin kamfen
A duka mazabu 171 da aka yi zaben kansila, a nan ma ‘yan jam'iyyar APC ne suka yi nasara.
EBSIEC ta yabi zaben kananan hukumomin Ebonyi
Enyi Patrick ya ce an yi zaben kananan hukumomin Ebonyi cikin zaman lafiya ba tare da an samu wani ya tada hatsaniya ba.
Babu jam’iyyar da ta shiga wannan zabe illa APC mai-ci, hakan ya nuna ba a ji kamshin sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayya ba.
Yaron Sanata David Umahi ya lashe zabe
Abin da ya fi jan hankali a zaben bai wuce nasarar Osborn Nweze Umahi, wanda mahaifinsa Ministan ayyuka ne a yau.
Gabanin rike kujerar minista, David Umahi wanda ya fito daga Ohaozara ya yi shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Ebonyi.
Da ya gama gwamna a 2023, ya koma Majalisar dattawa a matsayin sanata amma bai dade yana rike da wannan kujera ba.
Chibueze Osigwe (Ebonyi), Eze Paul Ituma (Ohaukwu), Chidi Henry Nwode (Ikwo) da Timothy Nwachi duk sun samu kujera.
Daily Post ta rahoto cewa Simeon Onuoha (Edda), Chidiebere Alo (Abakaliki), da Michael Anyim (Ivo) za su zama ciyamomin jihar.

Kara karanta wannan
"Na tausaya masa": Jigon PDP ya hango matsalar da za ta tunkari Tinubu idan ya yi tazarce
Jam'iyyar PDP ta soki zaben da aka yi
Jam’iyyar PDP ta reshen Ebonyi ta yi watsi da sakamakon wannan zabe da ya ba Osborn Umahi nasara a karamar hukumar Ohaozara.
Sakataren yada labaran PDP na reshen, Darlington Onwe ya kira taron manema labarai ya yi kaca-kaca da zaben da aka ce an yi.
Hon. Onwe ya ce EBSIEC da gwamnatin Ebonyi ba su shirya abin da za a kira zabe ba, ya ce abin da aka yi ya saba tsarin mulki.
Sanarwar murnar lashe zabe da Osborn Umahi ya fitar a Facebook.
Okorocha ya yi karar APC da INEC
Ana da masaniya Gwamnan Imo da APC za su yi shari’a da Rochas Okorocha. Tsohon gwamnan ya ce shi ne ‘dan takaran sanata a APC
Rochas Okorocha yana ƙalubalantar bayyana Gwamnan Imo a matsayin ɗan takarar sanata alhali wa’adinsa bai kare ba a kotu.
Hope Uzodinma yana so ya koma majalisa watanni gabanin karewar wa'adinsa domin da ba zai bar gidan gwamnati ba sai a 2028.
Asali: Legit.ng