Kwankwaso Ya Shawarci Yari game da Nema wa Tinubu Kuri'a a Zaben 2027
- Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki tsarin kwamitin yakin neman zaben APC ta 2027, yana cewa ya ƙunshi mutanen da suka goyi bayan gwamnatin yanzu
- Ya buƙaci Sanata Abdul’aziz Yari ya sake tunanin karɓar shugabancin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC da sake nazari game da goyin bayan Bola Tinubu
- Kwankwaso ya kuma 'diga ayar tambaya game da dacewar shigar manyan jami’an gwamnati tsarin tara kuɗin yaƙin neman zaɓen jam’iyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – 'Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya caccaki tsarin da APC mai mulki ta zo da shi gabanin 2027.
Kwankwaso ya soko kwamitin yaƙin enman zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC da aka kafa kwanan nan, inda ya ce ya nuna irin zaɓin da ke gaban ’yan Najeriya a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Ba tare da tsoro ba, Kwankwaso ya fadi rukunin mutane 2 da za su gwabza a zaben 2027

Source: Twitter
Kwankwaso ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, inda ya ce kwamitin ya haɗa da wasu daga cikin ’yan siyasar da suka goyi bayan gwamnatin yanzu, suka kare ta ko kuma suka taka rawa a cikinta.
Kwankwaso ya dura kan APC
A cikin sanarwar, Kwankwaso ya ce hakan ya haifar da muhimmiyar tambaya kan abin da APC ke son ’yan Najeriya su zaɓa a 2027, ko sabon tsarin mulki ne ko kuma ci gaba da tafiya da tsarin da ya ce ya jefa al’umma cikin matsanancin hali.
Kwankwaso ya ce a ganinsa, zaɓen 2027 zai zama fafata wa tsakanin talakawan Najeriya da waɗanda suka amfana, suka kare tare da ci gaba da tallafa wa tsarin da ya ce shi ne sanadin matsalolin da al’umma ke fuskanta.
Ya ce abin damuwa ne yadda iyalai a faɗin ƙasar ke fama da hauhawar farashin abinci da sauran muhimman abubuwan buƙata.
Kwankwaso ya jero matsalolin Najeriya
Ya ƙara da cewa matasan Najeriya na fuskantar rashin aikin yi da raguwar damarmaki, yayin da manoma da ’yan kasuwa ke ƙoƙarin tsira da rayuwa, sannan miliyoyin mutane ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro.
Kwankwaso ya ce bangaren ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyukan gwamnati ma na fuskantar matsananciyar matsala.
Ya ce tsarin yaƙin neman zaɓen APC ya sake nuna wani yanayi na fafatawa tsakanin “masu danniya da waɗanda ake zalunta.”

Source: Facebook
Sanata Kwankwaso ya yi kira ga ’yan Najeriya su yi amfani da zaɓen 2027 wajen ƙin ci gaba da abin da ya kira danniya da kuma neman shugabanci mai alhaki wanda ya fi mayar da hankali kan bukatun jama’a.
“Idan mutanen Osun za su iya yin hakan, sauran sassan ƙasar ma za su iya."
Kwankwaso ya kuma yi kira ga Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ya amince ya zama Darakta-Janar na kwamitin yajin neman zaben Shugaban Ƙasa a APC, da ya yi nazari sosai tare da sake tunanin karɓar wannan matsayi. Ya ce a matsayinsa na tsohon Gwamnan Zamfara kuma fitaccen ɗan siyasa daga Arewa maso Yamma, Yari ya san illolin rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, ƙaura da lalacewar hanyoyin samun abin dogaro da kai a shiyyarsa.
Kwankwaso ya tabo gwamnoni
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnonin da ke tunanin za su yi amfani da magudin zaɓe da ikon hukumomin jihohi domin ci gaba da mulki bayan 2027 za su sha kunya.
Tsohon gwamnan Kano ya ce rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi da tabarbarewar ayyukan gwamnati na iya shafar yadda masu zaɓe za su kada ƙuri’unsu a babban zaben da ke tafe.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ’yan Najeriya na ƙara waye wa a siyasance kuma za su iya ƙin zaɓen gwamnonin da ke neman komawa kan kujerunsu.
Asali: Legit.ng

