Gwamna Ya Halarci Taron Kungiyar Izala, Ya Ce Tallafin Tinubu na Isa ga Talakawan Najeriya

Gwamna Ya Halarci Taron Kungiyar Izala, Ya Ce Tallafin Tinubu na Isa ga Talakawan Najeriya

  • Gwamna Ahmed Aliyu ya ce tasirin manufofin Shugaba Bola Tinubu a rayuwar ’yan Najeriya a bayyane yake a ƙasar nan
  • Gwamnan ya ce gwamnatin tarayya ta samar da tallafin abinci, taki kyauta da sauran tallafi ga ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi
  • Aliyu ya yi kira ga ’yan Najeriya da su sake zaɓar Tinubu, yana mai cewa shugaban ba zai ba ƙasar kunya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi fatali da ikirarin ’yan adawa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai inganta rayuwar ’yan Najeriya cikin shekaru uku da suka gabata ba.

Gwamna Aliyu ya bayyana wannan ikirari na yan adawa a matsayin farfagandar siyasa, yana mai cewa tallafin da Tinubu ya bada na abinci da taki na iss hannun talaka.

Kara karanta wannan

Farfesa ya ɗauko tarihi, ya fadi yadda rasuwar Umaru Musa Yar'adua ta illata Najeriya

Ahmed Aliyu.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu a gidan gwamnatinsa Hoto: Ahmed Aliyu
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a wani taron yini ɗaya na ƙasa mai taken, “Inganta Siyasa da Adalci a Zamantakewa a Matsayin Maganin Haɗin Kai da Ci gaban Najeriya."

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ce ta shirya taron a Jos, Jihar Plateau.

“Idan ba ka ga tasirin Tinubu a rayuwar ’yan Najeriya ba, to ba a Najeriya kake ba ko kuma ka bar kasa,” in ji shi, yana mai cewa gudunmawar shugaban ƙasar ga al’umma a bayyane take.

Tinubu ya ba da tallafin abinci da taki

Aliyu ya ce bai kamata a ce gwamnatin Tinubu ba ta samar da tallafin abinci ko taimako ga ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi ba.

Ya ce:

“Mun san gaskiyar komai, duk wanda yake cewa ba a raba tallafin abinci, ko taimako ga ’yan Najeriya matalauta ba, to ba ya Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ban tsani Kiristoci ba"; Sheikh Jingir ya yi karin haske kan kalamansa

“Ya kamata mu san cewa abinci ya wadata. Mun san gwamnati ta bayar da taki kyauta. Mun san gwamnati tana bayar da tallafin da ya dace domin taimaka wa talakawa.

Gwamnan ya ƙara da cewa duk ayyukan da Tinubu ya aiwatar suna nan a bayyane, kuma ’yan Najeriya za su ga tasirinsu.

Gwamna Aliyu ya goyi bayan Tinubu

Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi la’akari da sake zaɓar Tinubu, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa shugaban ba zai ba ƙasar kunya ba.

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, Gwamna Umar Namadi na Jigawa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da sauran manyan baki sun halarci taron.

Sai dai ’yan adawa sun yi watsi da yadda gwamnatin ta kimanta nasarorin da ta samu a fannin tattalin arziki, kamar yadda Vanguadr ta ruwaito.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kaddamar da wasu ayyuka Hoto: @aonanuga1956/X
Source: Twitter

Gwamnan Sakkwato ya raba motocin yaki

Kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta yi rabon motoci yaki 62 tare da kayan aikin tsaro daban-daban ga jami'an tsaro da ke aiki a jihar.

Gwamna Ahmad Aliyu ya ce an yi haka ne a karkashin shirin Operation Fight Terrorism da nufin magance ta'addancin 'yan bindiga.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta ba wajen inganta harkar tsaro da kuma kula da rayuwar jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262