Kotu Ta Yanke Wa Babban Malamin Addinin Musulunci Hukuncin Daurin Rai da Rai, Ta Fadi Laifinsa
- Kotu a kasar Siriya ta yanke wa Sheikh Ahmad Badreddin Hassoun hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan kama shi da laifi
- Ahmad Hassoun, tsohon babban Muftin Syria, ya samu hukuncin daurin rai da rai kan laifukan da suka shafi yakin basasar kasar
- Hassoun, wanda ya rike mukamin babban limamin Siriya daga shekarar 2005 zuwa 2021, an kama shi a filin jirgin saman Damascus a watan Maris din 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Syria - Kotu ta yanke wa babban malamin addinin musulunci a kasar Siriya, Sheikh Ahmad Badreddin Hassoun hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
Sheikh Ahmad Badreddin Hassoun, shi ne tsohon babban limamin Musulmi na Siriya a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasar Bashar al-Assad.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa an yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa laifukan da ya aikata a lokacin yakin basasar kasar da ya shafe kusan shekaru 14.
Kotu ta kama Ahmad Hassoun da laifi
Kotun Laifuka ta Hudu da ke Damascus ce ta yanke hukuncin a yau Litinin, bayan ta same shi da laifuka da dama, ciki har da tunzura mutane, halasta kisa da kuma amfani da mukaminsa ba bisa ka'ida ba.
Hassoun, wanda ya rike mukamin babban limamin Siriya daga shekarar 2005 zuwa 2021, an kama shi a filin jirgin saman Damascus a watan Maris din 2025, bayan ya fito daga wurin buyarsa wata guda kafin hakan.
An fara shari'ar tasa ne a ranar 25 ga Yuni. Kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a wani bangare na laifuffukan, bayan ta same shi da laifin tunzura mutane zuwa kisa.
Laifuffukan da malamin ya aikata
Alkalin kotun ya kuma yanke masa hukuncin shekaru 10 a gidan yari bayan an same shi da laifin halasta kisan gillan da ake yi.
Kotun ta kuma umurci Hassoun da ya biya diyya domin rama wa wasu daga cikin wadanda ya cutar da hakkokinsu.
Alkalin kotun, Fakhr al-Din al-Aryan, ya ce an yi amfani da Hassoun da hukumar addinin da yake jagoranta wajen ba da kariyar addini ga ayyukan soji da jami'an tsaro a lokacin mulkin al-Assad.
Alkalin ya ce wa'azilozinsa sun kuma halasta amfani da bama-bamao da aka jefa kan wuraren da fararen hula ke zaune, lamarin da ya haddasa mummunar barna kuma ya saba wa dokokin kasa da kasa na jin kai.

Source: Getty Images
Kotu ta ƙi yiwa malamin sassauci
Kotun ta gano cewa Hassoun ya rika kira ga jami'an soji da sojojin kasar Siriya a cikin wa'azinsa da su tunkari 'yan adawar gwamnati.
Haka kuma, ya yi kira ga sojoji da su "shafe tare da lalata" wuraren da ake harba makamai daga gare su, tare da yin barazanar kisa da korar al'ummar Idlib.
Kotun ta tabbatar da cewa Hassoun ba zai amfana da wani afuwa ta gama-gari ko ta musamman ba, saboda girman laifuffikan da aka same shi da aikatawa.
Kotu ta yanke Bashar al-Assad hukunci
A wani labarin, kun ji cewa wata kotu ta samu tsohon shugaban Syria, Bashar al-Assad, da laifin kisan gilla, azabtarwa da kuma aikata laifuan cin zarafin bil’adama.
Bisa haka ne kotun ta yanke wa tsohon shugaban kasar da kaninsa, Maher al-Assad, hukuncin kisa bayn shafe tsawon lokaci ana fafata shari'a.
Asali: Legit.ng

