Amnesty Ta Shiga Batun Sace Masallatan da Ke Sallar Juma'a a Neja

Amnesty Ta Shiga Batun Sace Masallatan da Ke Sallar Juma'a a Neja

  • Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta ceto masu ibadar da aka sace yayin sallar Juma’a a Kpenya, Jihar Neja
  • Mazauna yankin sun ce sama da mutane 80 ne ake zargin an yi garkuwa da su, yayin da gwamnati ta ce har yanzu ana tantance adadin
  • Gwamnan Neja Mohammed Bago ya umurci jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen gano maharan da ceto mutanen da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gaggauta tabbatar da kubutar masu ibadar da aka yi garkuwa da su a wani masallaci a Jihar Neja.

An kai harin ne a ranar 21 ga Agusta yayin da musulmi ke gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Kpenya da ke gundumar Dekara, Ƙaramar Hukumar Borgu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake da wasu mutane

'Yan bindiga sun sace masallata a Kano
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

An sace masu ibada yayin sallar Juma’a

Amnesty International ta bayyana a wata sanarwaa cewa ba a bayyana takamaiman adadin mutanen da aka sace ba, cewar rahoton Premium Times.

Sai dai mazauna yankin sun yi zargin cewa sama da mutane 80 ne maharan suka yi awon gaba da su.

Ƙungiyar ta bukaci hukumomin Najeriya da su ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da sakin waɗanda aka sace tare da magance yawaitar hare-haren garkuwa da mutane a yankunan karkara na Arewacin ƙasar.

Amnesty ta ce abin damuwa ne musamman kasancewar an sace mutanen ne yayin da suke gudanar da ibadar sallar Juma’a.

Amnesty ta bayyana illolin garkuwa da mutane

Ƙungiyar ta ce wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga hare-haren garkuwa da mutane a baya sun bayar da rahoton fuskantar azabtarwa, yunwa, cin zarafin mata ta hanyar lalata da kuma yanke sassan jiki.

Ta kuma ce wasu waɗanda aka yi garkuwa da su an tilasta musu kallon ko kuma shiga cikin wasu munanan ayyukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

Amnesty ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace domin dakile yawaitar garkuwa da mutane a arewacin Najeriya.

Gwamnatin Neja ta tabbatar da harin

Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da faruwar harin ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Obed Nana.

Obed Nana ya ce wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari Masallacin Kpenya yayin da masu ibada ke gudanar da sallar Juma’a.

Ya ce harin ya shafi al’ummomin Gidan-Zana da Kpenya, inda wasu mazauna yankin suka tsere zuwa wuraren da ke kusa domin tsira.

Sai dai maharan sun yi awon gaba da wasu masu ibada, yayin da gwamnati ke ci gaba da kokarin gano ainihin adadin mutanen da aka sace.

Bago ya bayar da umarnin ceto waɗanda aka sace

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago, ya umarci jami’an tsaro da su ƙara kaimi wajen gano maharan da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Obed Nana ya ce an tura jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban domin tantance halin da ake ciki, bin sawun maharan da kuma gudanar da aikin ceto.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara, sun tura yan bindiga da dama lahira

Ya ce gwamnati ba za ta bayyana wasu bayanan aikin da za su iya kawo cikas ga kokarin ceto mutanen ba.

Gwamnatin ta kuma bukaci mazauna yankin da su guji yaɗa alkaluman da ba a tabbatar da su ba, tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen gudanar da aikin.

Amnesty ta bukaci a ceto masallata a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun sace basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga da yin garkuwa da Sarkin gargajiya na al’ummar Igbesi da ke karamar hukumar Isin ta Jihar Kwara.

'Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da wasu mazauna yankin, a wani mummunan hari da suka kai wa kauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng