Tsaro: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan zanga - zangar kungiyar CAN

Tsaro: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan zanga - zangar kungiyar CAN

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa halayyar kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) a 'yan kwanakin baya bayan nan ta tabbatar da cewa dukkan 'yan Najeriya suna da damar gudanar da zanga - zanga da kuma bayyana ra'ayinsu a kan harkokin da suka shafi addini da siyasa.

A jerin wasu sakonni da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya wallafa a shafinsa na sada zumunta (Tuwita), fadar shugaban kasa ta bayyana cewa CAN ta gudanar da zanga - zanga ne sakamakon kisan gillar da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa Fasto Lawan Andimi.

Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai ji dadin kisan Fasto Andimi ba, kuma ya mika sakonsa na ta'aziyya da jaje ga iyalin mamacin.

"Shugaban kasa da sauran hadimansa sun amince da salon zancen da CAN ta yi amfani da shi yayin zanga - zangarsu, watau 'dukkan wani rai, na Musulmi ko Kirista, yana da muhimmanci'.

"Musulmi ko Kirista, muna girmama addinin dukkan 'yan Najeriya kuma zamu kare hakkin kowa tare da tabbatar da cewa duk wani dan kasa yana da 'yancin gudanar da addininsa a duk inda yake zaune," a cewar Garba Shehu.

Tsaro: Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan zanga - zangar kungiyar CAN
Garba Shehu
Asali: Facebook

Kakakin ya cigaba da cewa, "a saboda haka, fadar shugaban kasa ta yi maraba da addu'o'in kungiyar CAN da kuma zanga-zangar da suka gudanar cikin lumana domin zaburar da 'yan kasa wajen ganin sun tashi tsaye domin hana aiyukan ta'addanci cigaba da faruwa a fadin kasa."

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada wa Lawan da Gbajabiamila a kan tsaro yayin ganawarsu

Garba Shehu ya ce akwai bukatar dukkan 'yan Najeriya su hada kai domin goyon bayan gwamnati da bata gudunmawa a kokarin da take yi na tabbatar da tsaro a fadin kasa.

A cewarsa, akwai wasu kungiyoyi dake yi wa gwamnati zanga-zanga sabanin su gudanar da zanga-zangarsu ga makiya gwamnati, wanda yin hakan tamkar nasara ce a wurin makiya da ke burin ganin sun yi amfani da addini domin haddasa fitina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel