Coronavirus: CAN ta yi umarni ga mabiyanta da su dakatar da al'amuran bauta

Coronavirus: CAN ta yi umarni ga mabiyanta da su dakatar da al'amuran bauta

- Yayin da cutar coronavirus ke ci gaba da kamari a kasashe da nahiyoyi, majami’ai suna ta daukar matakan shawo kan matsalar

- Kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta umarci cocina da su dakatar da al’amuran bauta

- Shugaban kungiyar na reshen jihar Kaduna ya shawarci cocina da ke jihar a kan su rage bauta idan ya zama dole ayi

A yayin da tsoron mugunyar cutar coronavirus ta ci gaba da yaduwa, kungiyar kiristoci ta kasa ta umarci mabiyanta da su dakatar da duk lamurran bauta da zai tara jama’a a waje daya.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito, kungiyar addinin ta bada sanarwar nan ne don a shawo kan yaduwar cutar a kasar nan.

Rabaren Joseph Hayab, shugaban kungiyar na jihar, wanda ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar, ya shawarci cocina da su rage ibadu ko kuma su gajarce lokacin ibadun idan ya zama dole ayi shi.

Hayab ya kara da bayyana wasu matakan kare kai daga cutar don mabiyan su kiyaye tare da gujewa samun cutar.

Babban faston ya kara jaddada umarnin cewa dole ne a taimaka wajen kare yaduwar cutar don haka a karanta shan hannu da rungumar juna.

Coronavirus: CAN tayi umarni ga mabiyanta da su dakatar da al'amuran bauta

Coronavirus: CAN tayi umarni ga mabiyanta da su dakatar da al'amuran bauta
Source: UGC

DUBA WANNAN: Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Ya kara da bayyana cewa kungiyar ta yarda cewa addu’a tana magani amma ba hanyar bullewa bace, idan yace mabiya su garzayo bauta ba tare da an kiyaye hanyoyin samun cutar ba.

Ya ce: “Kalubalen cutar coronavirus duk duniya ne kuma ta zama annobar da ta addabi kasashe masu yawa a fadin duniyar nan.”

“Don haka duk cocin da ke Najeriya kada su kuskura wajen nuna halin ko-in-kula ga wannan cutar. Cocin a matsayin wajen koyar da addini, an santa da tara jama’a don addu’a, biki, wa’azi da sauransu. Dole ne masu bauta su hada kai da gwamnati da ma’akatan lafiya don kare yaduwar cutar.” yace.

Takardar ta kara da tabbatarwa da gwamnatin Najeriya cewa CAN za ta hada kai da ita tare da cibiyoyin lafiya wajen ilimantarwa tare da wayar da kan ‘yan Najeriya wajen yakar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel