Gwamnonin arewa sun nuna bakin ciki kan kisan babban faston Adamawa

Gwamnonin arewa sun nuna bakin ciki kan kisan babban faston Adamawa

Kungiyar gwamnonin Arewa ta yi Allah-wadai da kisan Reverend Lawan Andimi, wanda ya kasance Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na gida kuma babban fasto a yankin Michika, jihar Adamawa wanda kungiyar yan ta’adda ta yi.

Gwamnonin arewa sun bayyana cewa sun yi bakin ciki matuka kan lamarin.

A Wani jawabi a Jos a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu, Shugaban kungiyar gwamnonin arewan kuma Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong ya bayyana lamarin a matsayin wani abun bakin ciki na rashin imani daga kungiyar yan ta’addan wacce ta yi kaurin suna wajen sanya radadi a zukatan yan Najeriya.

Yayinda ya ke ta’aziyya ga iyalan faston, coci da kuma mutanen jihar Adamawa, Lalong ya bukace su da kada su bari mummunan lamarin ya shafi imaninsu ga Allah da son mutane, kamar yadda mutuwar faston ba zai haddasa kiyayya a zukatan yan Najeriya ba.

Lalong ya jadadda cewa kungiyar gwamnonin arewa na nan tsayin daka wajen hada hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari don yakar kungiyar yan ta’addan

A wani labarinna daban, mun ji cewa cewa mazauna kauyen Jami da ke karamar hukumar Kanam ta jihar Plateau sun kasha wasu masu fashi da makami su biyar.

KU KARANTA KUMA: Matan Najeriya basu iya soyayya kamar Turawa ba – Isa Suleiman

Wata majiya daga yankin, wacce ta bayyana yadda lamarin ya afku, ta bayyana cewa mutanen kauyen Tumtum da ke karamar hukumar Kaman ne suka tsayar da masu fashin a wata mota kirar Peugeot 406 sannan suka kashe su bayan sun samu labarin cewa sun yi wa wata motar Bas kirar Toyota mallakar kamfanin taliya fashi a hanyar Wase-Kanam da ke karamar hukumar Kanam na jihar inda suke a hanyarsu ta dawowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel