Farfesa Ya Dauko Tarihi, Ya Fadi Yadda Rasuwar Umaru Musa Yar'adua Ta Illata Najeriya
- Farfesa Pat Utomi ya nuna cewa rasuwra marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'adua ta maida Najeriya baya
- Utomi ya ce da Umaru Musa Yar’Adua bai mutu yana kan mulki ba, da yanzu Najeriya ta wuce haka a fannin samun ci gaba
- Ya bayyana marigayi Shugaba Yar’Adua a matsayin ɗan kishin ƙasa na hakika kuma mai son ganin Najeriya ta ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Farfesan Tattalin Arziƙin Siyasa, Pat Utomi, ya ce da tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua bai mutu ba, da Najeriya ta zama “wata ƙasa ta daban.".
Utomi ya ce rasuwar Yar'adua ta maida Najeirya baya, yana mai cewa da ya rayu da kasar nan ta samu ci gaba fiye da yadda take a yanzu.

Source: Twitter
Farfesa Utomi ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri mai suna Csuite Cafe da aka wallafa a Youtube, inda ya bayyana marigayi Yar’Adua a matsayin “ɗan kishin ƙasa na gaskiya” wanda yake son ganin Najeriya ta samu ci gaba.
Utomi ya tuna tayin da Yar'dua ya masa
Yar’Adua ya rasu a ranar 5 ga Mayu, 2010, inda mataimakinsa a lokacin, Goodluck Jonathan, ya gaje shi a matsayin shugaban ƙasa.
Utomi ya ce a wani lokaci Yar’Adua ya gayyace shi zuwa fadar shugaban ƙasa tare da ƙoƙarin shawo kansa ya shiga majalisar ministocinsa.
Farfesan ya ce ya shaida wa marigayin shugaban cewa ya fi son bayar da shawarwari idan aka nemi shawararsa maimakon ya zama minista.
Sai dai Utomi ya ce Yar’Adua ya dage cewa zai iya yi wa ƙasar ƙarin amfani idan ya shiga gwamnati a matsayin minista fiye da kasancewarsa a wajen gwamnati.
Sai dai Utomi ya ce ya amsa masa cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne samun tasiri, ba wai shiga gwamnati kawai ba, kuma ba ya ganin zai iya samun tasiri a irin tsarin PDP na lokacin.
Yar'dua ya yi kokarin shawo kan Utomi

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Tun kafin lokaci, an kammala tsara wanda zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027
Sai dai Yar’Adua ya ce hakan bai isa ba, domin mutum na iya yin ƙarin tasiri daga cikin gwamnati fiye da abin da zai iya faɗa daga wajen gwamnati.
Utomi ya ce bayan Yar’Adua ya shafe wasu mintuna yana ƙoƙarin shawo kansa, sai ya gaya wa shugaban ƙasar cewa zai zama abin dariya idan ya shiga majalisar ministoci bayan ya riga ya kafa wata gwamnatin da za ta rika sa ido.
“Nigeria da ta zama wata ƙasa daban da Yar’Adua ya rayu. Ya kasance shugaban ƙasa mai kishin ƙasa na gaskiya.
“Wataƙila ya yi kuskure a nan da can, amma ɗan kishin ƙasa ne wanda yake son ganin Najeriya ta ci gaba,” in ji Utomi.
Shawarar da Utomi ya ba Yar'adua
Utomi ya ƙara da cewa daga baya ya ba da shawarar cewa zai bai wa shugaban ƙasar jerin sunayen mutane bakwai da za su iya yin aiki tare da shi domin ciyar da ƙasar gaba.

Source: Facebook
Ya ce ya aika da jerin sunayen zuwa ga Yar’Adua ta hannun Stephen Oronsaye, tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027
“Na koma na rubuta sunayen mutane bakwai daga sassa daban-daban na Najeriya waɗanda nake ganin suna da ƙwarewa kuma za su iya kawo sauyi,” in ji shi.
Utomi ya ce daga baya wani mutum ya shaida masa cewa Yar’Adua bai samu jerin sunayen ba, kuma wataƙila ya rasu yana tunanin cewa Utomi ya ƙi amincewa da buƙatarsa.
Obasanjo ya kare kansa kan Yar'adua
A wani labarin, kun ji cewa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana da masaniyar cewa marigayi Umaru Musa Yar'adua bashi da koshin lafiya kafin ya goyi bayansa.
Tsohon shugaban kasar ya musanta zargin cewa kutunguila da kitimurmura suka sanya shi bawa Yar'adua takara a 2007.
Asali: Legit.ng
