Dangote Ya Fadada Raba Man Fetur Kyauta Zuwa Kano da jihohi 3 a Najeriya

Dangote Ya Fadada Raba Man Fetur Kyauta Zuwa Kano da jihohi 3 a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa matatar Dangote da ke Legas ta faɗaɗa shirin raba man fetur da sauran kayayyakin man fetur kyauta zuwa jihohin Kano da sauransu
  • Kamfanin ya ce matakin zai rage kuɗin safarar man fetur ga ƴan kasuwar mai masu zaman kansu tare da samar da damar rage farashin man fetur ga jama'a
  • Ƙungiyar IPMAN ta yaba da shirin, tana mai cewa zai rage matsalolin kuɗi da na sufuri da 'yan kasuwar mai ke fuskanta a yayin da suke rarraba man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lagos – Matatar Dangote ta sanar da faɗaɗa shirin raba man fetur da sauran kayayyakin man fetur kyauta zuwa jihohin Kano, Imo da wasu jihohi biyu.

Matatar ta ce shirin zai rage kuɗin da 'yan kasuwar mai masu zaman kansu ke kashewa wajen safarar man fetur daga matatar zuwa wuraren da suke gudanar da kasuwancinsu.

Kara karanta wannan

Malamin addini da ke goyon bayan Tinubu ya magantu kan tallafin mai

Alhaji Aliko Dangote a wajen taro
Lokacin da Aliko Dangote ya yi bayani a wajen taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta rahoto cewa ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, inda ta ce shirin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage kuɗin rarraba man fetur.

Jihohin da shirin ya shafa

A farko, shirin ya shafi Legas, Ogun, Rivers, Kaduna, Abuja da Delta, kafin yanzu a ƙara Kano, Imo, Anambra da Nasarawa.

Matatar ta ce manufar shirin ita ce kusantar da kayayyakin man fetur zuwa ga ƴan kasuwa da masu sayar da su, tare da rage kuɗin safarar kayayyakin daga matatar zuwa wurare masu nisa.

This Day ta wallafa cewa kamfanin ya ce ta hanyar ɗaukar nauyin kuɗin kai kayayyakin, ana cire wani muhimmin ɓangare na kuɗin da ke cikin tsarin rarraba man fetur.

Fatima Aliko Dangote ta ce ya kamata a ga amfanin tace ɗanyen mai a cikin gida kuma ya kai ga 'yan kasuwa da masu amfani cikin sauki.

Kara karanta wannan

FBI na fargabar sakin bayanan zargin Tinubu a Amurka ya jawo babban hadari

IPMAN ta yaba da matakin

Ƙungiyar IPMAN ta yi maraba da matakin, tana mai cewa zai taimaka wajen rage matsalolin kuɗi da sufuri da ƴan kasuwar mai masu zaman kansu ke fuskanta.

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa kuma Jami'in Hulɗa da Jama'a na IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce shirin zai rage wahalhalun da ƴan kasuwa ke fuskanta wajen jigilar kayayyakin man fetur.

Matatar Dangote da ke Legas
Wani sashe na matatar Dangote. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Ya bayyana cewa a wasu lokuta ƴan kasuwa kan biya kuɗin kayayyaki amma su shafe kwanaki ko makonni suna jiran a loda musu su kuma kai su inda suke.

A cewar matatar Dangote, rage waɗannan kuɗi na iya bai wa ƴan kasuwa damar yin gogayya wajen farashin da suke sayar da man fetur ga jama'a.

Dangote ya ƙara farashin mai

A wani labarin, mun ruwaito cewa matatar Dangote da ke Legas ta ƙara farashin man fetur a wajen lodinta da N20 a kan kowace lita.

Farashin ya tashi daga N1,165 zuwa N1,185 kan kowace lita, inda sabon farashin ya fara aiki daga tsakar daren 21 ga Agusta 2026.

Rahoto ya nuna cewa karin farashin ya zo ne yayin da farashin ɗanyen mai na Brent ya haura $93 kan kowace ganga a kasuwar duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng