Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya sallami shuwagabannin tsaron Najeriya

Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya sallami shuwagabannin tsaron Najeriya

Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami kafatanin manyan shuwagabannin hukumomin tsaron Najeriya gaba dayansu sakamakon cigaba da tabarbarewar tsaro da ake samu a Najeriya.

Daily Trust ts ruwaito shugaban CAN na kasa, Samson Ayokunle ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis, 24 ga watan Janairu a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Kwankwaso na shirin dawowa APC don takarar shugaban kasa a 2023 – Ganduje

Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya sallami shuwagabannin tsaron Najeriya
Kungiyar kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya sallami shuwagabannin tsaron Najeriya
Asali: Facebook

Shugaban CAN ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi game da kisan shugaban kungiyar kiristoci, CAN, reshen jahar Adamawa wanda mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram ta dauki alkalin aikatawa.

Ayokunle yace ba daidai bane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cigaba da aiki da manyan hafsoshin tsaron Najeriya duba da gazawarsu wajen magance matsalolin tsaron Najeriya duk da dadewar da suka yi a wadannan mukamai.

Daga karshe Ayokunle yace zasu gudanar da azumi tare da addu’o’in samar da zaman lafiya a Najeriya dagaaranar 31 ga watan Janairu zuwa 2 ga watan Feburairu na shekarar 2020.

A wani labarin kuma, kotun duniya, watau International Court of Justice ta umarci gwamnatin kasar Myanmar da ta dauki matakan kare al’ummar Musulman kasar da ake kira Rohingya daga cin zarafin da ake musu tare da barazana ga rayuwarsu.

Haka zalika kotun ta umarci gwamnatin Myanmar ta tabbatar da kare rayuwar Musulman Rohingya tare da dukiyoyinsu, sa’annan ta tabbata ta adana duk wasu shaidu dake nuni da cin zarafi, wulalanci da kuma kisan gillar da aka yi ma Musulmai a baya.Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

Musulman kasar Gambia ne suka shigar da gwamnatin kasar Myanmar kara gaban kotun a watan Nuwambar da ta gabata biyo bayan kashe kashen da aka yi ma Musulmai a kasar, inda suke zargin Myanmar da aikata laifin kisan kare dangi tare da keta dokar majalisar dinkin duniya na 1948.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel