Ba Shekara 8 ba, Sarki Ya Bukaci a Bar Tinubu Ya Ci gaba da Mulkin Najeirya na Tsawon Lokaci

Ba Shekara 8 ba, Sarki Ya Bukaci a Bar Tinubu Ya Ci gaba da Mulkin Najeirya na Tsawon Lokaci

  • Mai marataba Sarkin Ibadan (Olubadan na Ibadan), Oba Rasheed Ladoja, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya cancanci ci gaba da mulki na dogon lokaci
  • Sarkin ya ce aikin hanyar Ibadan zuwa Ijebu na da muhimmanci wajen inganta tsaro da tattalin arzikin mazauna Ibadan da kewaye
  • Ladoja ya ce Tinubu ba jagoran jam'iyyar APC mai mulki kawai ba ne, illa shugaban Najeriya baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, Nigeria - Sarkin Ibadan (Olubadan na Ibadan) Oba Rasheed Ladoja, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya cancanci ci gaba da shugabancin Najeriya na dogon lokaci, yana mai kafa hujja da ayyukan gwamnatinsa.

Ladoja ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wajen bikin ƙaddamar da aikin faɗaɗa hanyar Ibadan-Ijebu mai layuka biyu a Jihar Ogun, inda Gwamna Dapo Abiodun ya wakilci Tinubu.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yi wa Tinubu yawa, jigon APC ya ba Atiku gaskiya kan dawo da tallafin fetur a Najeriya

Oba Rasheed Ladoja
Sarkin Ibadan da ke jihar Oyo, Oba Rasheed Ladoja Hoto: Aranni Yahaya
Source: Twitter

Olubadan ya fadi cancantar Tinubu

Sarkin ya ce bai kamata a ayyana taron a matsayin gangamin jam’iyyar APC ba, duk da yawan ambaton jam’iyyar da aka yi a wajen taron, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya ce:

"Na ji kowa yana magana APC, APC. Bola Tinubu ba mutumin APC ba ne, a’a. Bola Tinubu yana aiki kuma ya cancanci zama shugaban ƙasa na dogon lokaci.”

Ladoja ya ce babban dalilin taron shi ne nuna godiya ga Tinubu saboda amincewa da aikin hanyar, wadda ya bayyana a matsayin muhimmiyar hanya ga tsaro da walwalar tattalin arzikin mazauna Ibadan da kewayenta.

"Wannan ba gangamin APC ba ne. Taro ne da muka zo domin gode wa Mai Girma Shugaban Ƙasa saboda tabbatar da wannan aikin hanya," in ji shi.

Me ya sa hanyar ke da muhimmanci?

Ladoja ya ce hanyar ta dade tana fuskantar matsalolin tsaro, musamman satar mutane, yana mai cewa sake gina ta zai taimaka wajen inganta tsaro da sauƙaƙa zirga-zirga.

Kara karanta wannan

Duk da suna jam'iyya 1, Gwamna Radda ya yi maganar nadin da Tinubu ya yi maaa a kwamitin kamfen

Olubadan ya ce:

“Mu da muke Ibadan mun san cewa wannan ita ce hanya ɗaya a Ibadan da ’yan ta’adda ke yin garkuwa da mutane.”

A cewarsa, matakin da Tinubu ya ɗauka na aiwatar da aikin ya nuna damuwarsa kan rayuwar al’umma.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sarkin ya ƙara da cewa bai kamata a auna ayyukan shugaban ƙasar ta fuskar siyasar jam’iyya kawai ba.

“Ya cancanci fiye da a kira shi shugaban kasa na APC. Ba shugaban APC ba ne, shi ne shugaban Najeriya," in ji Olubadan.

Shin aikin zai taimaki APC?

Ladoja ya amince cewa irin ayyukan da Tinubu ke yi na iya ƙara wa APC damar samun nasara a zaɓuka masu zuwa.

Olubadan ya ce jam’iyyun siyasar da ke neman kalubalantar jam’iyyar mai mulki dole ne su shawo kan masu zaɓe cewa suna da damar samar da madadin shugabanci.

Ya ce sun yi imanin cewa Tinubu ya cancanci yin mulki na dogon lokaci, duk da cewa wasu jam’iyyun adawa na ta ƙoƙarin nuna cewa suna da tasiri.

Kara karanta wannan

An tono tarihi, rikicin Atiku ya jawo yunƙurin yi wa shugaban ƙasa juyin mulki a Najeriya

Tinubu zai cika alkawurran da ya dauka

Kun ji cewa daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban Ƙasa na APC, Abdul’aziz Yari, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa jam’iyyar za ta cika alkawuran da ta ɗauka a 2023.

Yari ya ce APC za ta ci gaba da tsayawa kan alkawuran da ta yi wa al’umma, yayin da take shirin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262