Tirkashi: 'Bible' din yanzu tatsuniyar gizo da koki ce - Ikhide Ikheloa ya caccaki Kiristocin Afirka
- Wani mutumi mai suna PA Ikhide yayi Allah wadai da 'yan Afirka da suke amfani da littafin Bible
- Ya bayyana cewa Bible littafi ne da aka rubuta shi akan karya da soki burutsu, littafi ne na tatsuniyar gizo da koki
- Ya ce lokacin da turawan da suka fara farautar bayi a Afirka, idan sun kama bayi da littafin suke yi musu addu'a kafin a sayar da su a wata uwa duniya
Ranar Litinin din nan ne Ikhide Ikheloa, wanda aka fi sani da PA Ikhide, ya caccaki mutanen yankin Afirka akan yadda suka yadda da littafin Bible.
Ikhide ya bayyana cewa "Bible rubutu ne kawai na tatsuniyar gizo da koki da wasu suka rubuta domin su dinga nishadantar da mata, da yara, da kuma wanda basu da aikin yi."
KU KARANTA: Kowa ya debo da zafi bakinsa: 'Yan coci sun yiwa Faston su dan karen duka
Ga abinda ya rubuta a shafinsa na Facebook:
"Bible littafin tatsuniya ne da wasu mutane suka kirkiro domin ya dinga debewa mata da yara kewa. Littafi ne da yake nuna wariyar launin fata, inda har ya kai ga turawa masu farautar bayi na wancan lokacin suna yin addu'a akan bayin da suka kamo a yankin Afirka ta Yamma kafin su sayar dasu.
"Abin yana bata min rai, idan naga cewa wai dan Afirka shine yake amfani da wannan littafi a matsayin abin yin bauta da shi. Muna da addininmu tun kafin zuwan turawa. Menene damuwar mu ne?"
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng