Leah Sharibu: Kungiyar al’ummar kiristocin Arewa ta mika muhimmin bukata ga Boko Haram

Leah Sharibu: Kungiyar al’ummar kiristocin Arewa ta mika muhimmin bukata ga Boko Haram

Kungiyar al’ummar kiristocin Arewacin Najeriya ta mika kokon bararta ga kungiyar ta’addanci na Boko Haram game da cigaba da rike wata daliba guda daya tak da suka sace tare da sama da dalibai dari daga makarantar yan mata ta Dapchi jahar Yobe.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar, Rabaran Yakubu Pam ne ya mika wannan bukata ga Boko Haram a madadin dalibar mai suna Leah Sharibu a ranar Juma’a 12 ga watan Oktoba, inda yace cigaba da rike yarinyar ya janyo tashin hankali ga iyayenta.

KU KARANTA: Wani babban jami’in gwamnati kuma na hannun daman Buhari ya rasu

“Munga ya dace mu janyo hankalin jama’a game da halin da ake ciki na satar wata daliba mai suna Leah Sharibu da sauran mutanen da aka sace, mun samu labarin maganan da yan ta’addan suka ce, don a haka a matsayinmu na shuwagabannin addinai muna magiya ga yan Boko Haram da su taimaka su saki Leah.

“Iyayenta da danginta sun sha kuka game da rashinta, kuma suna roko da a sako mata diyarsu, haka zalika yan Najeriya ma sun koka, kuma muma muna kira da sakota, don Allah ku sako yan matannan.” Inji Pam.

A watannin da suka wuce ne mayakan Boko Haram a karkashi jagorancin shugaban wani tsagi, Mamman Nur suka kai farmaki makarantar yan mata dake Dapchi, inda suka sace sama da yan mata dari, da dama daga cikinsu musulmai ne.

Sai dai bayan kwanaki kadan sai yan Boko Haram din da kansu suka lodo yan daliban a cikin motocinsu, suka dawo dasu har cikin garin Dapchi, sai dai sun bukaci daliba Leah Sharibu ta musulunta ta hanyar yin Kalmar shahada, amma ta ki, don haka suka mayar da ita daji suka cigaba da riketa.’

Amma Malaman musulunci da dama sun yi watsi da wannan mataki na Boko Haram, inda suka ce ba koyarwar addinin musulunci bane a tilasta ma mutum shiga musulunci, Allah mai tsarki da daukaka ya hana haka a Al-Qur’ani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel