'Integrity Group': Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Ba Zasu Yiwa Atiku Kamfen Ba

'Integrity Group': Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Ba Zasu Yiwa Atiku Kamfen Ba

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da sauran fusatattun gwamnonin PDP sun yi wata ganawa a jihar Legas
  • Da isarsu wajen taron, gwamnonin da ake yiwa inkiya da G-5 sun sanar da kafa sabuwar kungiya a cikin PDP mai suna ‘Integrity Group’
  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ne ya bayar da sanarwar kafin su shiga ganawar sirri da sauran jiga-jigan APC da suka hallara a jihar

Lagos - Fusatattun gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da aka fi sani da G-5 sun sanar da kafa sabuwar kungiya mai suna ‘Integrity Group’ wato kungiyar mutunci a cikin babbar jam’iyyar adawar a ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a yayin ganawar da tayi a gidan tsohon mataimakin shugaban PDP, Cif Olabode George, kungiyar ta ce babu gudu babu ja da baya a kan hukuncinta na kin shiga kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

2023: PDP Ta Yi Watsi da Gwamnonin G-5, Zata Ci Gaba Da Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa a Wata Jihar Arewa

Gwamnonin PDP
Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

Gwamnonin karkashin jagorancin Wike sun bukaci shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu yayi murabus domin adalci da daidaito, Daily Nigerian ta rahoto.

An bukaci Ayu ya sauka ne jim kadan bayan Atiku ya lashe zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baya ga Wike sauran gwamnonin kungiyar sun hada na jihar Benue, Samuel Ortom, Seyi Makinde na Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da kuma Okezie Ikpeazu na Abia.

Gwamnonin sun gana ne da wasu fusatattun shugabannin jam’iyyar adawar a jihar Legas domin sanin matakin da za su dauka.

Menenen sunan sabuwar kungiyar ta PDP?

Koda dai har yanzu babu cikakken bayani kan ganawar da suka yi a cikin sirri, ana ganin ba zai rasa nasaba da matsalar da ta dabaibaiye jam’iyyar PDP ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wike, Wasu Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Sun Sa Labule a Legas

Makinde wanda ya zanta da manema labarai kafin ya shiga cikin ganawar, ya bayyana cewa kungiyar ‘Integrity Group’ ita ke jan ragamar fafutukar da a cikin jam’iyyar.

Jawabinsa na cewa:

“Mun kasance a nan da safen nan don yin wata ganawa ta kungiyar ‘Integrity Group a cikin jam’iyyarmu, ta PDP. Ta kasance na kungiyar G5 wato gwamnonin PDP biyar. G5 ya kasance kungiyar ‘Integrity Group. Kuna iya ganinmu, gwamnoni biyar masu ci, a matsayin fuskokin wannan fafutuka amma shugabanni da dattawan jam’iyyar da kuka gani a nan sune a bayan wadannan fuskokin.
“Mun kasance a kudu maso yamma da safiyar nan don nazarin halin da ake ciki a jam’iyyarmu, don bitar inda muka kwana da kuma duba abun da zai faru a zabe mai zuwa. A karshen tattaunawarmu, za ku ji cikakken bayani kan inda muka tsaya a kan wadannan lamura. A dadain shugabanninmu da dattawa a kudu maso yamma, ina mai yiwa mambobin ‘Integerity Group’ maraba da zuwa.”

Kara karanta wannan

Wike Ya Sake Tada Kura, Ya Ce PDP Za Ta Gane 'Khaki Ba Leda Bane'

Asali: Legit.ng

Online view pixel