Nafiu Bala Ya Yi wa Atiku Sabon Isgilanci kan Takarar 2027 a ADC

Nafiu Bala Ya Yi wa Atiku Sabon Isgilanci kan Takarar 2027 a ADC

  • Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala Gombe ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya koma unguwarsa domin sake yin rajistar zama ɗan jam’iyyar
  • Nafiu Bala ya ce zai yi la’akari da naɗa Atiku a matsayin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC na 2027 idan ya kammala rajista
  • Wannan kira na zuwa ne yayin da rikicin shugabancin ADC ke ƙara tsananta, bayan INEC ta ce za ta jira hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kafin ɗaukar mataki kan takaddamar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban tsagin jam’iyyar ADC, Nafiu Bala Gombe ya yi kira ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya koma unguwarsa domin yin rajista a matsayin cikakken ɗan jam’iyyar.

Nafiu Bala ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da yake mayar da martani kan matakin da jam’iyyar za ta ɗauka bayan INEC ta ce za ta jira hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rikicin shugabancin ADC.

Kara karanta wannan

Matsala na neman tunkaro Atiku kan zaben 2027, kungiya ta mika bukatunta

Nafiu Bala Gombe
Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala. Hoto: Nafiu Bala
Source: Facebook

Kiran Nafiu Bala ga Atiku

A cikin sanarwar da kakakin tsagin, Christopher Okechukwu, ya sanya wa hannu, Punch ta rahoto Nafiu Bala ya buƙaci Atiku ya ajiye takaddamar da ke tsakaninsu, ya koma unguwarsa domin yin rajista.

Ya ce yin rajistar zai bai wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar damar more dukkan haƙƙoƙi da gata da cikakken ɗan jam’iyyar ke da su.

Nafiu Bala ya kuma bayyana cewa zai yi la’akari da naɗa Atiku a matsayin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC na 2027 idan ya kammala rajistar.

Ya ce gogewar Atiku a siyasa, saninsa a faɗin ƙasa da fahimtarsa kan harkokin mulki za su taimaka wa jam’iyyar wajen ƙoƙarin kayar da gwamnatin APC da samar wa ’yan Najeriya wata madadin shugabanci.

ADC ta shirya kamfen a 2027

Nafiu Bala ya bayyana cewa ɓangaren jam’iyyar ya gudanar da wani taron dabarun yaƙin neman zaɓe tare da ’yan takararsa na shugaban ƙasa, gwamnonin jihohi da Majalisar Tarayya.

Kara karanta wannan

Har yanzu Atiku na cikin jerin 'yan takarar shugaban ƙasa a shafin INEC? Bincike ya gano gaskiya

An gudanar da taron ne a cibiyar taro ta NCI International Conference Centre da ke Kaduna, domin daidaita shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen babban zaɓen 2027.

Taron ya samu halartar ɗan takarar shugaban ƙasar ɓangaren, Farfesa Chris Uba, da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Dakta Shamsuddeen Modibbo Barkindo, tare da sauran ’yan takara daga sassan Najeriya.

Atiku Abubakar
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya kuma buƙaci ’yan takarar da su koma mazabunsu, su ƙara wayar da kan jama’a da neman goyon baya a matakin ƙasa, tare da haɗa kai da shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai.

PDP ta soki hadakar 'yan adawa

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta ƙi amincewa da ikirarin cewa ta shiga ƙungiyar haɗakar jam’iyyun adawa da tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa, Salihu Lukman, ke jagoranta.

PDP ta bayyana cewa ba ta shiga wata yarjejeniya da ƙungiyar ba, kuma ba ta ba kowa izinin wakiltarta a taron da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Nuwamba, 2026.

Jam’iyyar ta ce Rainbow Coalition ce kaɗai haɗakar siyasa da ta amince da ita, bisa jagorancin jagoranta na ƙasa kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng