Nafisa Kwankwaso Ta Yi wa Abba Tas Ganin Gwamna Ya ‘Saki’ ‘Yaruwarsu wajen Taro
- Nafisa Musa Kwankwaso ta zama ‘yar cikin dangi ta farko da aka ji ta shiga batun matsalar auren Gwamnan Kano
- Lauyar ta zargi Abba Kabir Yusuf da rashin yi wa matarsa ta biyu adalci, ta tuna masa alherin da aka yi masa a baya
- A wani rubutu da ta yi, Nafisa Kwankwaso ta zargi Mai girma gwamna da cin mutuncin uban Zainab Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Nafisa Musa Kwankwaso ta shiga cikin maganar auren Mai girma Abba Kabir Yusuf da kuma Hajiya Zainab Musa Kwankwaso.
A yayin da ake ta tattaunawa game da matsalar auren, Nafisa Musa Kwankwaso ta fito ta yi wata magana da ta ke kama da hura wuta.

Source: Twitter
A shafinta na Facebook a ranar Talata 17 ga watan Nuwamba 2026, Hajiya Nafisa Kwankwaso ta yi wa Gwamnan jihar Kano kaca-kaca.
‘Yar uwar matar gwamnan da ake tunanin aurenta ya zo karshe ta nuna abin da ya faru bai yi mata dadi ba, kuma ba ta iya boye fushinta ba.
Nafisa Kwankwaso ta yi rubutu marasa dadi tana bayanin wahalar da ‘yaruwarta ta sha da Abba Kabir Yusuf a rayuwa tun kafin ya samu mulki.
Surukar Gwamnan jihar Kano ta yi masa gori
Duk da ba ita ta auri gwamnan jihar Kano ba, kwararriyar lauyar ta yi masa gorin cewa lokacin da ya auri Zainab Kwankwaso bai da gida.
A rubutun, ta tuna wa mai girma gwamna cewa yadda ya rika zama a gidan haya da uwar yaransa kafin a ba shi gida, har ya samu gwamnati.
Barista Nafisa ta ke cewa gabanin Abba Kabir ya shiga fadar gwamnati, uwar ‘ya ‘yansa ta zauna a cikin gidan a mulkin Rabiu Kwankwaso.
Sanata Rabiu Kwankwaso wanda yake tamkar ubansu ya yi gwamna sau biyu a 1999-2003 sai kuma tsakanin shekarar 2011 da 2015.
A wancan lokaci, Abba Kabir hadimi ne a wajen surukinsa, daga baya kuma ya zama kwamishinan ayyukan jihar Kano na kusan shekaru uku.
An zarge shi da cin mutuncin Rabiu Kwankwaso
Ta zargi surukin nasu da cin mutuncin tsohon gwamnan da kuma yin abin da mahaifiyarsa ba za ta so ba domin tana kaunar Hajiya Zainab.
Kafin ta kare, sai da ta tuna wa Gwamna Abba cewa Allah SWT ya azurta shi da ‘ya ‘ya mata kusan 10 a lokacin da yake maganar kara aure.
Lokacin da Abba ya yi wannan magana a kan mimbarin siyasa, lauyar ta ce abin da gwamnan ya yi, ya jefa duk wata mace a cikin takaici.
Abin da Nafisa Kwankwaso ta rubuta a Facebook
Ga cikakken abin da ta wallafa a shafinta:
Abba Kabir Yusuf
Kaji kunya, ka fadi babu nauyi. Babu macen da zata aure ka ta shekara 20 da kai cikin talauci da wahala da yawon gidan haya, tana ta maka biyayya tana kare mutuncinka kuma sai da ka zama wani abu ace taje kotu neman saki, kai kam ina mamakin wane irin bala'i kasa ta a ciki. Tun kafin ta aure ka ta zauna a wannan gidan da kake taqama dashi yanzu kana ganin babu uban da ya isa dakai, a matsayin 'yar gwamna, sanda ta aureka Babanta Minister ne Abba, tay ta binka gidan haya bayan gidan haya har ta kai matsayin da shi wanda kake kira tsulan yace ga gida nan kaje ka zauna saboda yaranka, amma yanzu shi kake kira yana tsilla tsilla saboda baka da kunya bakada mutunci. Abba kaji kunya, ka zubarwa da kanka mutunci, ka raina muslunci ka raina mahaifiyarka dake matukar kainar Zainabu. Abin tausayi gashi Allah ya jarrabeka da yara mata kusan goma. Kai da kake taqama zaka qara aure duk wata mace da tasan abinda take yau tana cikin alhini, babu uban da ya san darajar mahaifiyarsa da zai dauki 'yarsa ya baka.

Kara karanta wannan
Kano ta ɗauki zafi, Gwamna Abba ya yi kalaman da ake zargin ya nuna ya saki matarsa
Salihu Yakasai ya yi tir da aikin Abba
An ji tsohon dan takaran gwamnan Kano ya tono abubuwan da suka faru tsakanin Abba Kabir Yusuf da matarsa, Zainab Musa Kwankwaso.
Salihu Tanko Yakasai ya yi rubutu a shafinsa yana cewa tun kafin gwamna ya bar jam'iyyar NNPP ya rika samun matsala da matarsa ta biyu.
Tsohon hadimin na Abdullahi Ganduje ya ji takaicin abin da ya faru, yake cewa bai kamata Abba ya tsinka igiyar aurensa a irin wannan yanayi ba.
Asali: Legit.ng

