Nima Peter Obi Zan Yi, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom Ya Bayyana

Nima Peter Obi Zan Yi, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom Ya Bayyana

  • Da alamun rikicin dake gudana a jam'iyyar PDP zai kaita ta fuskanci matsala a zaben shugaban kasa a 2023
  • Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya yi kira ga jama'a suyi watsi da jam'iyyanci, shi dai Peter Obi zai yi
  • Peter Obi dai shine dan takarar kujerar shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar yan kwadago

Benue, Makurdi - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP abin zabi, rahoton Vanguard.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda Peter Obi ya kai masa ziyarar jaje bisa annobar ambaliya da ta afkawa al'ummar jihar a kwanakin nan.

Ortom yace Peter Obi mutum ne mai halin kirki, gaskiya da kuma aminci.

Ya ce Obi ne mutumin da yan Najeriya ke bukata don gyara kalubalen da kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Fi Atiku Alheri, Shi Zamu Yi A Abia: Dan takara Gwamna na PDP

Peter Obi
Nima Peter Obi Zan Yi, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom Ya Bayyana
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ce yan Najeriya suyi watsi da kabilanci da bangaranci na jam'iyya saboda yanzu shugaban kwarai ake bukata.

A cewarsa:

"Saboda haka, mu ajiye jam'iyyanci a gefe mu hada karfi da karfe wajen ceto kasar nan."
"Najeriya ba tada lafiya. Na fada kuma ina maimaitawa, muyi dubi cikin manyan yan takara 3 don ganin wanda zai kawo sauyi kasar nan."
"Najeriya na bukatar shugaba mai hangen nesa, tunani da kuzari kuma Obi ne mutumin."

Peter Obi Ya Fi Atiku Alheri, Shi Zan Yi: Cewar Babban Jigon PDP

Dazu mun kawo muku cewa wani cikin yan takaran kujerar gwamnan jihar Abia a zaben fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sampson Orji, ya bayyana cewa Peter Obi na jam'iyyar LP zai goyi baya a zaben shugaban kasa.

Orji ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Alhamis a Umuahia, birnin jihar Abia, rahoton PremiumTimes.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Ya bayyana cewa ya fifita Peter Obi kan Atiku Abubakar na PDP ne saboda dan takaran na LP ya fi na PDP kwarewa.

Hakazalika yace zai taya Peter Obi yakin neman zabe.

A cewarsa:

"Har gobe ina PDP, amma Obi zai goyi baya, ba dan Inyamuri bane amma saboda abinda yake waklta. Iyali na da abokaina shi zasu zaba."
"Atiku aboki na ne, amma Obi ya fi shi alheri. Sabanin iyawa da akafi Atiku, adalci shine a zabi Obi."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel