Idan ka isa, mu yi fito na fito – Gwamna ya kalubalanci Wike, ya kira shi ‘dan giya’ a fili

Idan ka isa, mu yi fito na fito – Gwamna ya kalubalanci Wike, ya kira shi ‘dan giya’ a fili

  • David Umahi ya maida martani bayan Gwamna Nyesom Wike ya ce shi ne ya jawo kotu ta tsige shi
  • Gwamnan jihar Ebonyi ya zargi Wike da facaka da dukiyar talakawa, har yana alfahari da hakan
  • Umahi ya kira abokin aikinsa da sunaye marasa dadi, kuma ya kalubalance shi ga yin mukabala

Ebonyi - Ana zargin Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bayyana takwaransa na jihar Ribas Nyesome Wike a matsayin maras ilmi, mai yawan shan giya.

David Umahi ya yi wannan bayani ne a lokacin da manema labarai suka yi hira da shi a makon nan. Gidan talabijin na AIT ya tsakuro bangaren tattaunawar.

Gwamna Umahi ya maidawa Nyesom Wike martani ne bayan ya fito yana shaidawa Duniya cewa shi ne ya taso shi a gaba, har kotu ta sauke shi daga kan mulki.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Da yake jawabi na raddi, gwamnan na Ebonyi ya ce abokin aikinsa yana yi tamkar shi ne Ubangiji.

Ni ba na shan giya - Umahi

PM News ta ce mai girma gwamnan ya ce bambancinsa da Wike shi ne sabanin addini, kuma shi ba ya dirkar giya. Baya ga wannan, ya ce Wike ‘danuwansa ne.

A farkon jawabinsa, Umahi ya ki kama sunan gwamnan da yake yi wa wannan martani. Amma daga baya sai ya fito a mutum, ya ce kowa ya ji maganar Wike.

Gwamnan Ebonyi
Gwamna Dave Umahi Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin kunya ne inji Gwamna

“Kun ji a tashar Channels TV ya na cewa shi ne sanadi. Mutumin da ya dogara da Ubangiji domin ya samu numfashi. Ina tausayin jahilici. Abin kunya!”
“Ka na takamar cewa ka tunbuke wani gwamna? Da wani matsayin? Saboda kurum ka na tattara dukiyar al’umma, ba don ka na da wata kwakwalwa ba.”

Kara karanta wannan

Ban Damu Da Tsige Ni Da Kotu Ta Yi Ba Ko Kaɗan, Har Ƙiba Da Kyau Na Ƙara, Gwamna Umahi

“Ka na dumbuzar kudin jama’a, kuma ka na tunkaho da wannan. Baya ga wannan, wanene kai?”

Umahi yana matashi ya yi arziki

“Ina shekara 25 na zama Biloniya. Duk rayuwa ta aiki na ke yi, kuma na kalubalance shi (Nyesome Wike) da ya fito mu yi mukabala a bainar jama’a.”
“Ba na kaddamar da titin kilomita 3.4. Titi mai tsawon kilomita 35 na ke kaddamarwa da tagwayen gadoji da manyan ayyuka.” – David Umahi.

Rikicin Obaseki da Wike

A kwanaki kuma an ji cewa Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya ɗauki zafi game da kalaman da ake ganin sun wuce gona da iri da gwamnan Ribas ya yi.

A kan haka Gwamna Obaseki ya yi kira ga uwar jam'iyyar PDP ta nemi Wike ya shiga taitayinsa. Hakan ya biyo bayan gorin sauya-sheka da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Asali: Legit.ng

Online view pixel