Atiku, Peter Obi Sun Gamu da Tasgaro a Yunkurin Tunkarar Tinubu da Murya Guda
- Wataƙila maganar dunƙulewar jagororin hamayya wuri guda domin yaƙar APC a zaeben 2027 ba zai tabata ba
- Atiku Abubajar yana neman mulki a ADC yayin da Peter Obi ya dage zai yi takara a ƙarƙashin jam'iyyar NDC
- ‘Dan takaran ADC ya ce maganar cewa ya yafe takara ba gaskiya ba ce, duk an gaza samun wanda ajiye burinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ƙoƙarin haɗin kan 'yan adawa domin gabatar da ɗan takara guda da zai fafata da Shugaba Bola Tinubu ya sake fuskantar wani babban koma-baya.
An samu matsala a sakamakon bambancin ra'ayi tsakanin magoya bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da na Mista Peter Obi.

Source: Twitter
Wasu yaran Atiku Abubakar sun bi Peter Obi
Rahoton Leadership ya ce an gagara samun jituwa har yau dangane da wanda zai yarda ya jingine burinsa, ya mara wa guda ya tunkari APC.
Wata ƙungiyar Coalition of Atiku Support Groups Initiative ta fitar da sanarwar canza layi a siyasa, yanzu ta koma goyon bayan takarar Obi/Kwankwaso.
Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum irinsu Isaac Fayose sun nuna cewa wannan lamari na iya zama share fagen janyewar Atiku daga takara.
Wasu sun yi hasashen cewa za a iya jin sanarwar janyewar a hukumance a taron haɗin kan 'yan adawa da aka shirya gudanarwa ranar 30 ga Nuwamba.
Ranar ake sa ran jam'iyyun da ke cikin shirin haɗaka za su tattauna game da fitar da ɗan takara guda da za su mara wa baya ya samu mulkin Najeriya.
Atiku Abubakar ya kore labarin janye takara
A ranar Lahadi, Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa ya janye takararsa ta shugaban ƙasa domin mara wa Peter Obi baya a zaɓe mai zuwa.
Alhaji Atiku ya bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya ta yaudara, mugunta da kuma rashin kunya.

Kara karanta wannan
Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai
Haka kuma, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar ADC, Dele Momodu, ya yi watsi da hasashen cewa Atiku zai janye bi bayan su Obi.
A wata sanarwa, Momodu ya nanata cewa ‘dan takaran yana da gogewa sosai kuma yana da muhimmanci a siyasa da ba zai rabu burinsa saboda NDC ba.
Ana so jam'iyyun adawa su tsaida mutum 1
Jaridar ta ce ko da akwai bambancin alƙibla, dukkan 'yan takarar da jam'iyyunsu na cikin ƙoƙarin samar wa 'yan adawa da ɗan takara guda gabanin zaɓe.
Sauran jam'iyyun da ke cikin wannan shiri sun haɗa da tsagin PDP, APM, PRP da kuma jam’iyyar SDP.
Ƙungiyar Coalition for Democracy, ƙarƙashin jagorancin tsohon jigo a APC, Salihu Lukman, ce ke jagorantar shirin samar da ɗan takara guda a 2027.
Sabuwar taƙaddamar nan ta kunno kai ne kwanaki kaɗan bayan da ƙungiyar ta ɗage taronta na biyu daga ranar 23 zuwa 30 ga watan Nuwamba, 2026.
Bayanai sun nuna an yi haka ne sakamakon buƙatar da wasu jam'iyyun da ke cikinta suka gabatar.
A lokacin sanar da hakan, Lukman ya ce dukkan jam'iyyun da ke cikin shirin sun yarda a soke duk wani kamfe ranar 30 ga Nuwamba domin a halarci taronsu.
Jam'iyyar NDC tana so Atiku ya yafe takararsa
Darekta Janar na kamfen NDC, Ibrahim Abdulkarim, ya yi kira ga Atiku da ya shiga ƙawancen da ke mara wa Obi/Kwankwaso baya domin kauda APC.
Abdulkarim ya bayyana cewa ba lallai ne ƙawancen ya kasance ƙarƙashin jam'iyyar adawa ta ADC ba.
Abin da bayanin shugaban yakin takarar Obi ya nuna shi ne har yanzu babu wanda ya shirya ajiye batun neman mulki tsakanin jam'iyyun ADC da NDC.
Akwai matsala a PDP da wasu jam'iyyu
A wani ɓangaren kuma, ɓangaren PDP da Tanimu Turaki ke jagoranta ya nuna kyakkyawan fata cewa ƙawancen 'yan adawa zai samar da ɗan takara guda.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na wannan tsagi, Ini Ememobong, ya ce ɓangarensu na cikin shirye-shiryen haɗin kan da ake yi, kuma ana sa ran nasara.
Bangaren Nyesom Wike da ya tsaida Sandy Onor dama ya nuna babu ruwansu da zancen kamar yadda Punch ta ruwaito har suna shirin kai kara a kotu.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Jigo a APC ya hango abin da zai hana Atiku samun kuri'un 'yan Arewa
Haka kuma kam’iyyar Democratic Leadership Alliance (DLA) ta nisanta kanta daga shirin ƙawancen, ta nuna ba ta yanke shawarar shiga cikin maganar ba.
A sanarwar da Shugabanta, Samuel Memeh, ya sanya wa hannu, DLA ta ce masu shirya ƙawancen sun yi mata bayani amma ba ta kai ga gamsuwa ba.

Source: Getty Images
'Yan takarar shugaban kasa za su yi muhawara
Za a ji cewa an gayyaci Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu 'yan takaran zuwa muhawarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
Za a gudanar da muhawarar ne ranar 10 ga Janairu, 2027 a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.
Masu shirya taron sun ce manufar ita ce bai wa 'yan Najeriya damar tantance manufofi da shirye-shiryen 'yan takaran da za su ba amanar kuri'unsu.
Asali: Legit.ng

