Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa

  • 'Dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana Gwamna Ifeanyi Okowa matsayin abokin tafiyarsa
  • Duk da kwamitin shawari ta zabi Gwamna Wike na jihar Ribas, an gano cewa Atiku ya sakankance cewa Wike bayan kaunarsa
  • Har ila yau, wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP, ba su aminta da Gwamna Wike ba ganin irin kusancin da kujerar take da ta shugaban kasa

FCT, Abuja - Atiku Abubakar, 'dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai gabatowa.

Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP a ranar Laraba ya zabi Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, a matsayin wanda zai kasance mataimakin 'dan takarar shugabancin kasan.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gwamna ya dura hedkwatar PDP don a tantance shi ya tsaya takara da Atiku

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa
Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar ya Zabi Gwamna Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa. Hoto daga arise.tv
Asali: UGC

Mambobin NWC sun yi zabe inda Wike ya samu kuri'u 13 yayin da Okowa ya samu uku kacal, lamarin da yasa masu ruwa da tsakin suka aminta da Wike.

Sai dai, Atiku Abubkar na gano ya kasa sakin jiki da Wike a matsayin abokin tafiyarsa sabodaya sakankance cewa gwamnan baya kaunarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike yayi wa Aminu Waziri Tambuwal aiki a zaben fidda gwani na 2019, duk da kuwa cewa Atiku ya zo ya lashe zaben, Arise Tv ta ruwaito.

Wasu manya a PDP an gano ba su aminta da Wike ba saboda tsananin kusancin mataimakin shugaban kasa da kujerar shugabancin kasan.

Ya sanar da zabinsa ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar PDP ta lasa dake Abuja. Ya ce ya yanke wannan shawarar ne bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Wike Ya Lashe Zaben Kwamitin Shawari Na Zaben Mataimakin Atiku a PDP

A cewarsa, hukunci ne mai tsauri gare shi wurin yankewa duba da irin nagartattun mutanen da aka shawarcesa ya zaba daga ciki.

"Ina farin cikin sanar da sunan Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin 'dan takarar shugaban kasa. Ina hango tafiyar da kasar mu, tare da dukkan 'yan Najeriya da kuma gina zaman lafiya, hadin kai da cigaba ga kowa," ya wallafa a shafinsa na Twitter.

2023: Wike Ya Lashe Zaben Kwamitin Shawari Na Zaben Mataimakin Atiku a PDP

A wani labari na daban, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi nasarar lashe zaben da majalisar shawara da PDP ta kafa domin taimakawa wurin zabo abokin tafiyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Daily Trust ta rahoto cewa, majalisar ta yi karamin zaben ne ga mutum ukun da aka gabatar da sunayensu domin saukake wahalar da ake ta sha wurin zakulo wanda ya cancanta a yi tafiyar da shi.

Kara karanta wannan

Akwai ƙura: Ibo sun buɗa wuta, sun ce bai dace Atiku ya dauki Wike a Jam’iyyar PDP ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng