"Tikitina Ya Fi na Obi da Kwankwaso"; Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kawo Dalilinsa

"Tikitina Ya Fi na Obi da Kwankwaso"; Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kawo Dalilinsa

  • Seyi Makinde ya ce haɗin gwiwar siyasa tsakanin Kudu maso Yamma da Arewa na daga cikin manyan dalilan da ya sa tikitinsa ya dace da shugabancin Najeriya
  • Ya bayyana gogewarsa a mulkin Oyo, ƙarfinsa na matashi da shirinsa na haɗin kan ƙasa a matsayin abubuwan da ke bambanta takararsa
  • Makinde ya ce a shirye yake ya jagoranci gwamnatin wucin gadi ta haɗin kan ƙasa, amma ba zai ci moriyar sakamakon wannan gwamnati ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM), Seyi Makinde, ya bayyana dalilan da ya sa yake ganin ’yan Najeriya ya kamata su zaɓi tikitinsa a zaɓen 2027.

Makinde ya kwatanta tikitinsa da na Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, inda ya ambaci haɗin gwiwar siyasa tsakanin Kudu maso Yamma da Arewa, gogewarsa a mulki da shirinsa na haɗa kan ƙasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga rikicin Ibrahim Masari, Gwamna Radda da 'yan APC, ya bayar da umarni

Makinde ya yi magana kan cancantarsa
Gwamna Seyi Makinde na jihar Borno a ofis Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin The Rooftop Podcast.

Makinde ya yi magana kan haɗin kan Arewa da Kudu

Gwamnan ya ce haɗin gwiwar siyasa tsakanin Arewa da Kudu maso Yamma ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya a lokutan da ƙasar ta fuskanci manyan ƙalubale.

A cewarsa, tikitinsa na da damar ci gaba da wannan al'ada ta haɗin kai, wadda ya ce ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiyar ƙasar, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Makinde ya yi nuni da juyin mulkin soja na farko a Najeriya, inda ya ce mutanen Arewa da Kudu maso Yamma sun kasance cikin waɗanda suka fi fuskantar asara.

"Baya ga haɗin gwiwar siyasa tsakanin Kudu maso Yamma da Arewa, wannan haɗin kai ya kasance yana samar da kwanciyar hankali ga Najeriya a lokutan rikici a baya.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya kalubalanci Atiku kan shirin dawo da tallafin fetur

“Idan aka koma ga juyin mulkin soja na farko a Najeriya, mutanen da aka kashe sun fi yawa daga Arewa da Kudu maso Yamma, domin a kodayaushe waɗannan yankuna suna kan gaba wajen ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiyar ƙasar.” In ji shi.

Ya yi magana kan gogewarsa a mulkin Oyo

Makinde ya kuma ambaci ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a jihar Oyo a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ya kamata ’yan Najeriya su yi la'akari da takararsa.

Ya ce gogewarsa a shugabanci, ƙarfinsa da yake ganin yana da shi a matsayinsa na matashi, da kuma manufofinsa na siyasa, za su taimaka wajen tafiyar da ƙasar.

Ya bayyana cewa shirinsa ya ginu ne kan alkawuran da za a iya tantancewa, domin ’yan Najeriya su samu damar yi masa hisabi kan abubuwan da ya yi alƙawarin aiwatarwa.

A cewarsa, bai kamata ’yan siyasa su dogara kawai da jawabai da alkawuran kamfen ba, dole ne a samu abubuwan da jama'a za su iya amfani da su wajen tantance ayyukansu.

Makinde ya yi bayanin shirin gwamnatin haɗin kan ƙasa

Ɗan takarar na APM ya kuma bayyana shirin kafa gwamnatin wucin gadi ta haɗin kan ƙasa, wadda zai yi amfani da ita wajen tunkarar matsalolin siyasa da tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

Ya ce a shirye yake ya jagoranci irin wannan gwamnati, amma ba zai ci moriyar sakamakon ayyukanta ba bayan kammala wa'adinta.

Makinde ya bayyana cewa idan yana da burin cin moriyar abin da gwamnatin za ta samar a nan gaba, hakan na iya shafar yadda zai yanke muhimman shawarwari.

“Zan iya jagorantar ta, amma ba zan kasance cikin waɗanda za su ci moriyar sakamakonta ba. Domin idan ina tunanin zan amfana da abin da zai biyo baya, hakan na iya shafar hukuncina da kuma yadda zan yanke wannan shawara.” In ji shi.

Ya ce matsalar tsaro ta shafi dukkan Najeriya

Makinde ya ƙara da cewa kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa ya zama dole saboda matsalar rashin tsaro da sauran abubuwan da ke haddasa ta ba su tsaya a wani yanki na Najeriya ba.

Ya ce matsalolin da ƙasar ke fuskanta suna buƙatar haɗin kai da fahimtar juna tsakanin yankuna domin samun mafita mai ɗorewa.

A cewarsa, shirin gwamnatin haɗin kan ƙasa zai ba da damar tunkarar waɗannan matsaloli ta hanyar samun matsaya guda tsakanin al'ummar ƙasar.

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Makinde ya yi magana kan Obi da Kwankwaso
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Makinde ya magantu kan takara a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya kare matakin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ya ce Kudu maso Yamma na iya samar da ’yan takarar shugaban ƙasa fiye da ɗaya ba tare da hakan ya cutar da muradun yankin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng