2027: Kusoshin Jam'iyyar NDC da Aka Rabu da Su alhali Peter Obi Yana tsakiyar Kamfe

2027: Kusoshin Jam'iyyar NDC da Aka Rabu da Su alhali Peter Obi Yana tsakiyar Kamfe

Abuja - Manyan jam’iyyun siyasa sun yi harama wajen ganin sun tunkari babban zabe mai zuwa na shekarar 2027 a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Sai dai jam’iyyar hamayya ta NDC tana fama da wasu matsaloli daga shiga takara, kafa kwamitin zabe zuwa wasu shari’o’i a kotu.

Peter Obi
Peter Obi da jagororin NDC a Imo Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Legit Hausa ta duba wasu ‘yan siyasa da suka watsa wa jam’iyyar NDC kasa a ido, suka sauya sheka ko suka daina goyon bayanta

Akwai kuma wadanda jam’iyyar ce ta kore su domin sun gano ba su tare da ita a zaben 2027.

Rahoton nan ya tattaro tsofaffin masu takara da shugabanni a jam’iyyar adawar a Najeriya da za su yi wa wata jam’iyyar aiki.

Manyan NDC da suka rabu da jam'iyyar

1. Mohammed Bunu

A ranar 25 ga watan Oktoba 2026, wasika ta fito daga jam’iyyar NDC cewa an kori Mohammed Bunu mai takarar majalisa a Borno.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun rutsa 'yan islamiya a jihar Neja an sace dalibai ‘yan mata

Mataimakin shugaban NDC a Borno, Umar Fema ya ce an kori Bunu daga jam’iyyar ne saboda yana tallar Atiku Abubakar a jihar.

Kafin hakan ta faru da shi, Bunu yana neman wakiltar birnin Maiduguri a Majalisar dokoki.

2. Joseph Danjuma

Shi Joseph Danjuma ya hutar da jam’iyyar hamayyar domin shi da kan shi ya rubuta takarda yana mai sanar da ita ya yi murabus.

Sakataren yada labaran na NDC ta reshen jihar Nasarawa ya fake da cewa ba a ba shi damar yin ayyukansa na kakakin jam’iyya ne.

Danjuma yana goyon bayan ‘dan takaran SDP ne a zaben gwamnan 2027, babu ruwan shi da Musa Shugaba-Abdulahi na NDC.

3. Yakubu Ochefu

Farfesa Yakubu Ochefu ya fito ya sanar da cewa bai amince da sunan shi da aka sa a kwamitin yakin neman zaben NDC a 2027.

Babban malamin da ke karantar da tarihin tattalin arziki a jami’ar Rev. Fr. Moses Orshio Adasu ya ce sam shi ba ‘dan jam’iyyar ba ne.

Vanguard ta rahoto Yakubu Ochefu yana cewa tun farko an maka sunan shi a ‘yan majalisar kamfe ba tare da an tuntube shi ba.

Kara karanta wannan

PRP ta yi kaca kaca da shirin Tinubu, ta taɓo batun kisan Sheikh Yahaya Masussuka

4. Felix Wilson

Ana ji ana gani Felix Wilson ya rabu da jam’iyyar NDC bayan ana murnar ya samu takarar ‘dan Majalisar dokoki a jihar Bayelsa.

Ya ce NDC ta canza sunansa da na Michael Magbisa wajen neman kujerar Sagbama II a Majalisar Bayelsa alhali shi ya ci zabe.

Sabon mataimakin gwamnan jihar Baylesa, Dr. Peter Akpe ya karbe shi tare da wasu tsofaffin ‘ya ‘yan jam’iyyar NDC a ofishinsa.

5.Saheed Umar

Saheed Umar rabuwa ya yi da jam’iyyar NDC duk da ya taba zama mataimakin shugabanta a karamar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa.

‘Dan siyasar ya zabi ya shiga jam’iyyar APC mai rike da mulki da ya raba jiha da Sanata Seriake Dickson wanda shi ne jagoran NDC na kasa.

Da ya tashi sauya-sheka, ya dauke su Gilbert Alawei, Agidi George, Azibola Oru, Solomon Etor, Fineman Eseimokumo da Munteuma Clifford.

5. Ibrahim Kashim

Shi Ibrahim Kashim yana takarar gwamna a Bauchi a inuwar NDC sai aka ji labarin ya yi murabus daga jam’iyyar da ta tsaida shi.

Kara karanta wannan

'Ba dalilin zaɓenka ba kenan': Ƴan Najeriya sun fusata da Tinubu ya je Makka addu'a

Tsohon sakataren gwamnatin jihar ya rabu da jam’iyyar NDC ba tare da ya yi wa magoya baya da masoya bayanin dalilin shi ba.

NDC ta gamu da koma-baya a kokarin ta na yakar APM, APC, PRP da sauran jam’iyyu a zaben gwamna da za a yi a Bauchi a badi.

Peter Obi
'Yan takaran NDC a zaben shugaban kasa, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

Na hannun daman jagoran NDC ya shiga APC

An samu labari lokacin da wani na kusa da Seriake Dickson ya rabu da NDC zuwa APC da jin an soke masu rajista a kotu.

Hukuncin kotu ke da wuya tun a watan Yunin 2026 aka ji Fyneman Wilson ya shiga APC daga jam’iyyar NDC mai adawa.

Hon. Wilson yana cikin wadanda ake ganin cewa a jihar Bayelsa, Seriake Dickson yana takama da su sosai a harkar siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng