2027: Magoya Bayan APC Sun Yi Takansu da Rigima Ta Ɓarke a Wurin Yakin Neman Zaben Gwamna

2027: Magoya Bayan APC Sun Yi Takansu da Rigima Ta Ɓarke a Wurin Yakin Neman Zaben Gwamna

  • An samu hatsaniya yayin ƙaddamar da kamfen din neman sake zaɓen Gwamna Uba Sani a filin wasa na Kaduna Township ranar Alhamis
  • Matasa waɗanda ke ɗauke da sanduna da wasu makamai, sun tayar da hankalin magoya bayan jam’iyyar APC da sauran waɗanda suka halarci taron
  • Wasu ’yan jarida sun rasa na’urorinsu yayin rikicin, amma jami’an tsaro sun shiga tsakani tare da korar matasan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - An samu hatsaniya yayin ƙaddamar da yakin neman sake zaɓen Gwamna Uba Sani a 2027 a Jihar Kaduna ranar Alhamis.

An samu barkewar hatsaniya ne bayan wasu gungun matasa masu hamayya da juna sun yi arangama a filin wasa na Kaduna Township Stadium. Rikicin ya sa wasu magoya bayan APC ciki har da mata, suka ruga don tsira da rayukansu.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya fara garkuwa da mutane a Amurka, 'yan sanda na neman shi

Jaridar Daily Trust ta lura cewa wasu matasa sanye da rigunan T-shirt masu launin rawaya, ɗauke da sanduna da wasu makamai, sune suka tada rikicin, lamarin da ya tayar da hankalin magoya baya da sauran waɗanda suka halarci taron.

Ba a bayyana ko su wane ne matasan ko kuma manufar zuwansu wurin taron ba amma lamarin ya fara ne yayin da Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Tajudeen Abbas, ke gabatar da jawabinsa a wajen taron.

An kuma ruwaito cewa wasu ’yan jarida da ke ɗaukar rahoton kamfen ɗin sun rasa wasu kayan aikinsu, ciki har da makirufoni, yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga wurin rikicin.

Daga bisani, jami’an tsaro da aka girke a wurin sun shiga tsakani tare da korar matasan, inda suka dawo da zaman lafiya a wani ɓangare na filin taron, lamarin da ya ba da damar ci gaba.

Shigar jami’an tsaron ya ba Gwamna Uba Sani damar gabatar da jawabinsa, inda wasu ’yan takara suka kewaye shi yayin da yake miƙa musu tutocin jam’iyya, kafin ya bar wurin.

Wani mamban APC da ya shaida faruwar lamarin ya gaya wa Daily Trust cewa rikicin ya ɓarke ne lokacin da matasan suka kutsa wurin taron ɗauke da makamai, suka fara kai wa juna hari.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

“Ba mu san ko su wane ne ko kuma abin da ya jawo rikicin tsakaninsu ba. An shiga ruɗani a ko’ina yayin da suka fara kai wa juna hari,” in ji shi.

A cewarsa, shugaban majalisar ya samu damar kammala jawabinsa, sannan aka raka shi zuwa kujerarsa kafin aka ci gaba da taron.

Ya ƙara da cewa gwamnan ma ya samu damar gabatar da jawabinsa tare da miƙa tutocin jam’iyya ga ’yan takarar kafin ya bar wurin.

Wani bidiyo da ke nuna yadda rikicin ya faru ya bazu sosai a shafukan sada zumunta.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, bai samu damar amsa kiran waya ba domin jin ta bakinsa kan lamarin har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Gwamnatin Kaduna ta karyata hana ADC taro

Kun ji cewa Gwamnatin Kaduna ta karyata cewa ta hana jam’iyyar ADC amfani da filin wasa na Ranchers Bees domin gudanar da gangaminta na ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamba, 2026.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Sadiq Mamman Lagos, ya ce wasikar da ake yadawa ta hana wurin taron ta karya ce kuma ba ta fito daga wurin su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262