‘Dan Takaran Gwamna Ya Watsa wa NDC Kasa a Ido da Ya Fice daga Jam’iyya Ana cikin Kamfe
- Ibrahim Muhammad Kashim, dan takarar gwamnan Bauchi na jam’iyyar NDC a zaben 2027 ya bar ta a makon jiya
- ‘Dan siyasar ya yi murabus daga jam’iyyar, yana cewa ya yanke shawarar ne bayan nazari mai zurfi da ya yi
- Kashim ya gode wa shugabannin NDC da mambobinta bisa damar da suka ba shi ta kasancewa cikin jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Bauchi - Jam’iyyar NDC ta gamu da babban kalubale a Bauchi domin kuwa ‘dan takaran gwamna ne ya rabu da ita.
Ibrahim Muhammad Kashim ya yi murabus daga NDC da ta ba shi tikiti a matsayin ‘dan takaran gwamna a jihar Bauchi.

Source: Facebook
'Dan takaran gwamnan NDC ya rabu da jam'iyya
A jaridar Leadership aka samu labari cewa Barr. Ibrahim Kashim ya bar NDC, yanzu bai cikin ‘ya ‘yanta a hukumance.
‘Dan takaran ya rubuta wasika yana sanar da murabus dinsa tun ranar 16 ga watan Oktoba.
A takardar da ya aika wa shugaban NDC na karamar hukumar Bauchi, ya ce matakin ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba.
Meyasa Ibrahim Kashim ya bar jam'iyyar NDC?
Kashim yake cewa ya yi murabus ne a kashin kan sa bayan ya dauki lokaci yana nazari.
Ya ce:
“Ina mai gabatar da murabus dina daga jam’iyyar Democratic Congress (NDC), daga ranar da aka rubuta wasikar nan.
Na yanke wannan shawara ne bayan yin nazari mai zurfi, kuma zabi ne na kai na. Ina godiya ga shugabancin jam’iyyar da mambobinta bisa damar da suka ba ni ta kasancewa cikin NDC.”
Tashar Channels ta ce Kashim ya gode wa shugabanni da ‘ya ‘yan jam’iyyar da suka ba shi damar kasancewa da NDC a rayuwarsa.
Ana so NDC ta cire shi daga rajista
‘Dan siyasar ya bukaci jam’iyyar ta san da wannan mataki da ya dauka kuma ta sabunta bayanan da ta ke da shi game da shi.
Yake roko cewa:
“Don haka, ina rokon a karɓi takardar murabus dina tare da sabunta bayanan jam’iyyar yadda ya kamata. Ina mika gaisuwata ta musamman gare ku,”

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan daba ɗauke da makamai sun kewaye jigon APC, sun kashe shi nan take
- in ji shi.
Kashim wanda ya kasance sakataren gwamnatin Bala Mohammed yana cikin ‘yan takaran gwamna 15 da INEC ta saki sunayensu.
An shirya cewa shi da Tata Alhaji za su yi wa NDC takarar gwamna a Bauchi a shekarr 2027.
Doka ta amince a canza 'dan takara?
Bayani daga shafin Lawglobalhub na masana shari’a ya nuna jam’iyyu za su iya canza ‘yan takara inda wadanda aka tsaida suka bar ta.
Sashe na 33 na dokar zabe ya yarda a canza mai takara idan har wanda aka ba tuta ya mutu ko kuwa ya yi murabus daga jam’iyyarsa.
Yanzu kallo zai koma wajen jam’iyyar adawa da NDC domin ganin ta kawo wanda zai canji Kashim a Bauchi tun da ya yi sallama da ita.

Source: Facebook
An karyata Babachir a batun takarar Osinbajo
An ji rahoto Laolu Akande ya ce Muhammadu Buhari ya sha nuna goyon bayansa ga burin Yemi Osinbajo na samun takara a APC a 2022.
Kakakin farfesan ya karyata ikirarin Babachir Lawal cewa marigayin bai so mataimakinsa ya gaje shi a mulki ba ganin Bola Tinubu ya fito.
Akande ya ce kalamai da ayyukan Buhari a 2022 sun nuna cewa bai hana Osinbajo neman tikitin zama 'dan takaran shugaban kasa ba.
Asali: Legit.ng

