An kuma samun shugaban da ya yi watsi da jam’iyyar NDC ya bi ‘dan takara na dabam

An kuma samun shugaban da ya yi watsi da jam’iyyar NDC ya bi ‘dan takara na dabam

  • Kakakin yaɗa labaran NDC na reshen jihar Nasarawa, Joseph Danjuma, ya yi murabus daga jam’iyyar adawar
  • Ya ce zai goyi bayan takarar tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu a zaɓen gwamnan jihar
  • Danjuma ya danganta murabus ɗinsa da rashin ba shi damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata a NDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Nasarawa - Sakataren yaɗa labarai na NDC ta reshen jihar Nasarawa, Joseph Danjuma, ya yi murabus daga jam’iyyar.

Joseph Danjuma ya bayyana goyon bayansa ga takarar tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu.

Obi NDC
'Dan takaran shugaban kasa, Peter Obi da jagoran NDC, Seriake Dickson a Abuja Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Kakakin jam'iyyar NDC ya bar ta a Nasarawa

Punch ta ce a zaɓen gwamnan jihar Nasarawa na 2027, Joseph Danjuma zai bi bayan Mohammed Abubakar Adamu a SDP.

Danjuma ya bayyana matakin nasa a cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban NDC na jihar a ranar 27 ga Oktoba 2026.

Kara karanta wannan

Wike ya faɗi abin da zai hana Obi zama shugaban ƙasa, ya tuna mummunan halinsa 1

Ya ce ya yanke shawarar barin NDC ne saboda rashin ba shi damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata a matsayin kakaki.

A cikin wasiƙar, ya ce:

“Ina miƙa murabus ɗina daga kasancewa mamba da kuma Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Jihar Nasarawa, ba tare da bata lokaci ba.”

Dalilin barin NDC ya goyi bayan M.A Adamu

Danjuma ya nuna cewa rashin damar gudanar da aikinsa na kakakin jam’iyyar a jihar ne ya sa ya zabi ya canza layi a siyasance.

‘Dan siyasar ya bayyana cewa yanzu zai shiga yaƙin neman zaɓen tsohon IGP, zai taimaka masa ya samu nasara a zaɓen gwamna.

‘Dan jaridan ya taɓa aiki da kafafen yaɗa labarai na rediyo, talabijin da jaridu kafin shigowa cikin siyasa.

Bayan haka, ya taɓa zama babban sakataren yaɗa labaran tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa, Damishi Luka Barau.

A zamanin yau na siyasar haɗin gwiwa, ya ce mutum na iya ci gaba da kasancewa a jam’iyyarsa amma ya bi wani ɗan takaran.

2027: Kungiyar mutanen Alago za ta yi SDP

Kara karanta wannan

Bayan zargin son Pantami, Wike ya magantu kan taimakon wani dan takara

Sun shirya wani gangamin siyasa domin nuna goyon bayansu ga takarar M. A Adamu ƙarƙashin ƙungiyar Alago Support Group.

Vanguard ta ce a nan Danjuma ya bayyana cewa sun kafa ƙungiyar ne domin shaida wa duniya inda ya sa gaba a takarar 2027.

Ya ce al’ummar Alago suna son su taka rawa wajen yanke makomar jihar Nasarawa a shekar badi.

Ya ce bayan nazari kan tarihin Adamu da irin hidimar da ya yi wa ƙasa, sun gamsu cewa ya cancanci jagorantar Nasarawa.

Danjuma ya kuma bayyana cewa Adamu ba baƙo ba ne ga al’ummar Alago, domin yana da alaƙa da su ta nasaba da jini.

Ya ce tsohon IGP ɗin ya yi karatu tare da wasu fitattun ’ya’yan yankin na Alago a Obi, sannan yana da dangantaka da yankin.

Sannan ya ce lokaci ya yi da al’ummar Alago za su daina zama masu kallo kawai yayin da ake maganar wanda zai mulki Nasarawa.

Nasarawa
'Dan takaran gwamnan jihar Nasarawa a SDP, Muhammad A. Adamu Hoto: Mohammed Abari
Source: Facebook

Peter Obi ya koya wa APC hankali

Jam'iyyar APC za ta ƙara ƙaimi wajen neman ƙuri’u saboda gudun a kara kunyata Bola Tinubu a Legas kamar yadda aka samu labari.

Kara karanta wannan

Atiku ko Tinubu: An raba gardama kan dan takarar da ya fi dacewa ya zama shugaban kasa

Peter Obi, ya samu kuri’u 582,454, yayin da ‘dan takaran APC ya tashi da 572,606 a zaben shekarar 2023 a garin da ya yi gwamnan jiha.

APC ta yi wa mambobi kusan miliyan 1 rajista, Musiliu Obanikoro yana sa ran za su zabi Tinubu da Kadri Hamzat a zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng