Farfesa Ya Kunyata NDC Ta Su Kwankwaso da Obi bayan Ganin Sunansa a Kwamitin Kamfe

Farfesa Ya Kunyata NDC Ta Su Kwankwaso da Obi bayan Ganin Sunansa a Kwamitin Kamfe

  • Farfesa Yakubu Ochefu ya yi magana kan naɗin da aka yi masa a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC
  • Tsohon sakataren ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya ya ce ba a tuntube shi ba, kuma bai amince a saka sunansa cikin jerin mambobin kwamitin ba
  • Ochefu ya bayyana cewa muƙamansa na shugabancin ANUA da Ochetoha K’Idoma sun wajabta masa kasancewa ba tare da nuna goyon bayan wata jam’iyyar siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - Farfesa Yakubu Ochefu, malamin tarihin tattalin arziki da nazarin dabarun siyasa a Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi, ya ƙi amincewa da naɗin da aka yi masa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC.

Farfesan ya bayyana hakan ne bayan da jam'iyyar NDC ta fitar da sunayen mambobin kwamitin yakin neman zabenta na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi: Rigima ta kunno kai baya kafa kwamitin yakin neman zaben NDC

Farfesa ya ce NDC ba ta tuntube shi ba
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026.

Farfesa Ochefu ya bayyana cewa ba ɗan jam’iyyar NDC ba ne, kuma ba a tuntuɓe shi kafin saka sunansa cikin jerin mambobin kwamitin.

Ochefu ya ce bai san da batun ba

Farfesan, wanda ya taɓa zama babban sakataren ƙungiyar shugabannin jami’o’in Najeriya (CVCNU), ya ce hankalinsa ya kai ga wani jerin sunayen da ke yawo a kafafen sada zumunta, mai taken kwamitin yaƙin neman zaɓen ƙasa na NDC.

A cikin jerin sunayen mambobi 155 da aka fitar ranar Lahadi, an saka sunan Ochefu a matsayin ɗaya daga cikin​ waɗanda za su shiga kwamitin.

Sai dai ya bayyana cewa bai taɓa kasancewa ɗan jam’iyyar NDC ba, kuma bai bayar da izininsa na shiga kwamitin ba.

"Ina so na sanar da jama’a cewa ba ɗan jam’iyyar NDC ba ne, kuma ban taɓa kasancewa ɗan jam’iyyar ba.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Akume: Babba a gwamnatin Tinubu ya bayyana makiyan Arewa

Ya ƙara da cewa ba a tuntube shi kafin saka sunansa cikin jerin, kuma bai amince da hakan ba.

Ya aika da sako ga shugaban kwamitin

Farfesa Ochefu ya bayyana cewa ya riga ya rubuta wa shugaban kwamitin wasiƙa domin ƙin amincewa da naɗin da kuma neman a cire sunansa daga jerin.

Ya ce ya kuma buƙaci a sake fitar da sabon jerin sunayen mambobi wanda ba zai ƙunshi sunansa ba.

A cewarsa, matakin ya zama dole domin kauce wa fahimtar cewa yana da alaƙa da jam’iyyar ko kuma ya amince da shiga harkokinta na siyasa.

Ya ce baya goyon bayan kowace jam'iyya

Farfesa Ochefu ya bayyana cewa muƙamansa na shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban jami’o’in Najeriya (ANUA) na kasa da kuma shugaban ƙungiyar Ochetoha K’Idoma suna buƙatar ya kasance ba tare da nuna bambancin siyasa ba.

Ya ce mambobin ƙungiyoyin biyu sun fito ne daga jam’iyyun siyasa daban-daban, don haka bai dace ya nuna goyon baya ga wata jam’iyya ta musamman ba.

Sanarwar tasa ta zo ne bayan fitar da jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC, inda aka saka sunansa ba tare da izininsa ba, a cewarsa.

Kara karanta wannan

Shettima ya kama sunan Atiku a taron APC, ya yi masa tonon silili

Farfesa ya ki shiga kwamitin NDC
Taswirar jihar Benue, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shettima ya soki Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi.

Kashim Shettima ya bayyana cewa babu wani abu na musamman da zai iya gabatar wa ’yan Najeriya baya ga ambaton alkaluman tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng