Jam'iyyar NDC Ta Kori Dan Takararta kan Zargin Tallata Atiku Abubakar

Jam'iyyar NDC Ta Kori Dan Takararta kan Zargin Tallata Atiku Abubakar

  • NDC a Borno ta kori Mohammed Bunu, ɗan takararta na Majalisar Dokokin jihar, bisa zargin tallata ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar
  • Jam’iyyar ta ce hotunan Bunu da Atiku, tare da tambarin ADC da taken “Sabon Tafiya, Sabon Salo”, sun jawo zargin cin amana ga NDC
  • A cewar wasiƙar korar, an gayyaci Bunu sau biyu domin ya kare kansa, amma rahoton jam’iyyar ya ce bai halarci zaman ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Jam’iyyar NDC a Jihar Borno ta kori ɗaya daga cikin ’yan takararta na Majalisar Dokokin jihar, Mohammed Bunu.

Jam'iyyar NDC ta kori dan takarar ne bisa zargin shiga yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar.

An kori dan takarar NDC a Borno
Jagoran jam'iyyar NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson Hoto: @IamHSDickson
Source: Facebook

A cikin wasiƙar korar da aka rubuta ranar 25 ga Oktoba, 2026, mataimakin shugaban NDC na jihar, Umar Fema, ya sanar da Bunu matakin da jam’iyyar ta ɗauka a kansa, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Bayan ƙarewar wa'adin INEC, ina makomar Pantami da Gwarzo da sauransu?

Wasiƙar ta bayyana cewa halin da ake zargin Bunu da shi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, dokokinta da ƙa’idojin ladabtarwa.

Hotunan Bunu da Atiku sun jawo matsala

A cewar wasiƙar, lamarin ya shafi wasu kayan yaƙin neman zaɓe da ke ɗauke da tambarin ADC, taken “SABON TAFIYA, SABON SALO”, da hotuna da sunayen Atiku Abubakar da Mohammed Bunu.

Jam’iyyar ta ce bayyanar hoton Bunu da sunansa a kan kayan yaƙin neman zaɓen ya haifar da tambayoyi kan alaƙarsa da ADC, biyayyarsa da kuma jajircewarsa ga NDC.

Fema ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar sun ɗauki lamarin a matsayin babban laifin ladabtarwa da ya kamata a bincika bisa kundin tsarin jam’iyyar da hanyoyin da take bi wajen warware irin waɗannan matsaloli.

An ce Bunu bai halarci zaman kare kansa ba

Wasiƙar ta ce shugabannin NDC na mazabar Hausari sun gayyaci Bunu domin ya bayyana a gabansu da misalin ƙarfe 10 na safe ranar 23 ga Oktoba, 2026, don ya mayar da martani kan zargin shiga ayyukan yaƙin neman zaɓen wata jam’iyya.

Kara karanta wannan

Matsala sabuwa ta tunkaro gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Sai dai, a cewar rahoton da shugabannin mazabar suka gabatar, Bunu bai halarci zaman ba domin ya kare kansa.

Bayan rashin halartar tasa, sakataren mazabar, Rabiu Umar, ya ba da shawarar ɗaukar matakin ladabtarwa, sannan ya miƙa batun ga kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a Majalisar Ƙaramar Hukumar Maiduguri Metropolitan Council (MMC).

An sake gayyatar Bunu a ranar 24 ga Oktoba domin ya bayyana a gaban kwamitin bincike, amma wasiƙar ta ce rahoton jam’iyyar ya nuna cewa bai halarci wannan zaman ma ba.

Shugabannin jam’iyyar sun amince da korar

Bayan nazarin rahoton kwamitin, shugaban NDC na MMC, Adamu Ibrahim, ya amince da shawarar korar Bunu tare da miƙa batun ga shugabancin jam’iyyar na jiha domin ɗaukar matakin gaba.

Umar Fema ya ce shugabancin NDC na jihar ya yanke shawarar korar Bunu ne bisa zarge-zargen da aka bincika da rahotannin da aka gabatar ta tsarin ladabtarwar jam’iyyar.

NDC ta kori dan takararta a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Batun Atiku zai janyewa Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani rahoto ya nuna cewa wai Atiku ya ce zai janyewa Peter Obi takara idan Rabiu Kwankwaso ya janye daga matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC.

Bincike bai tabbatar da iƙirarin cewa Atiku ya ce zai janyewa Obi takara idan Kwankwaso ya bar matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng